Jerin Jiga-Jigan PDP Da Shugaban Kasa Bola Tinubu Ya Bai Mukami
Jim kadan bayan nasarar Shugaban Kasa Bola Tinubu a babban zaben 2023, ana ta rade-radin cewa yana shirin kafa gwamnati ta hadin kan kasa ta hanyar nada wasu yan siyasa masu adawa mukamai.
Daga baya shugaban kasar ya ce ya fi sha'awar kafa gwamnati da za ta yi aiki don gina kasar.
Sai dai kuma, yanayin mutanen da shugaban kasar ya ba mukamai tun bayan rantsar da shi ya tabbatar da rade-radin da aka dunga yi a baya.
Ya fara da nada Nyesom Wike, tsohon gwamnan jihar Ribas, a matsayin ministan Abuja, Shugaban kasa Tinubu ya nada wasu mambobin jam'iyyar adawa ta eoples Democratic Party (PDP) a gwamnatinsa.
Ga jerin sunayen wasu daga cikinsu:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
1. Nyesom Wike - Ministan Abuja
Wike, wanda ya ki goyon bayan dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, a zaben 2023 saboda rikicin cikin gida, ya yarda cewa ya yi wa Tinubu aiki.
Harma an yi masa takwici da mukamin minista.
2. Chiedu Ebie - shugaban NDDC
A kwanan nan ne shugaban kasa Tinubu ya nada sabon kwamitin gudanarwa na hukumar raya yankin Neja Delta (NDDC).
Kamar yadda jaridar PM News ta rahoto, shugaban kwamitin, Chiedu Ebie mamba ne a jam'iyyar PDP a lokacin da aka sanar da nadin nasa.
An rahoto cewa tsohon Gwamna James Ibori wanda ya kasance aminin shugaban kasa Tinubu ne ya taimaka wa Ebie wajen samun mukamin.
3. Monday Igbuya, wakilin Delta a kwamitin NDDC
Rahotanni sun kuma kawo cewa wakilin jihar Delta a kwamitin NDDC, Monday Igbuya, ma dan PDP ne.
Ana kuma zargin cewa Ibori ne ya taimaka wajen nadin nasa.
4. Victor Kolade Akinjo, wakilin Ondo, a kwamitin NDDC
Wakilin jihar Delta a kwamitin NDDC,Victor Kolade Akinjo, shima dan PDP ne.
Akinjo, tdohon dan majalisar wakilai kuma dan PDP ya sha kaye a kokarinsa na komawa majalisa a karo na uku inda dan takarar APC ya yi nasara.
5. Boma Iyaye, NDDC
Shugaban kasa Tinubu ya nada Boma Iyaye, dan PDP a jihar Ribas, a matsayin babban daraktan harkokin kudi na NDDC.
Bomo ya kasance akawu kuma tsohon kwamishinan wasanni a karkashin tsohon Gwamna Wike, ministan Abuja mai ci.
Na yi mamakin nada ni ministan Abuja, Wike
A wani labarin, mun ji cewa Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya Abuja, ya bayyana cewa nadinsa ba abu ne da ya sa rai ba.
Da yake jawabi a wata hira da Channels TV a ranar Laraba, 30 ga watan Agusta, tsohon gwamnan na jihar Ribas ya bayyana cewa ya yi mamaki lokacin da ya samu labarin nadin nasa a matsayin ministan Abuja.
Asali: Legit.ng