Rikicin Cikin Gida: Uwar Jam’iyya Ta Bayyana Matsayin Rabiu Kwankwaso a NNPP

Rikicin Cikin Gida: Uwar Jam’iyya Ta Bayyana Matsayin Rabiu Kwankwaso a NNPP

  • Rabiu Musa Kwankwaso ya na nan a matsayin ‘Dan jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, har gobe
  • Majalisar NEC ta ce ‘dan takaranta na shugaban kasa shi ne fuskar NNPP, babu wanda zai kore shi
  • Shugaban NNPP, Mallam Kawu Ali ya ce wadanda su ka dakatar da Kwankwaso ‘yan taware ne

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Majalisar NEC ta koli a jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, ta yi maganar matsayin ‘dan takararta a zaben 2023, Rabiu Musa Kwankwaso.

Vanguard ta ce Majalisar ta nuna Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ne fuskar jam’iyya mai alaman kayan dadi, saboda haka ba a za a iya yin waje da shi ba.

Rabiu Musa Kwankwaso ne ya tsaya takarar shugaban kasa a karkashin NNPP, yanzu ana fama da rigingimu har wasu na ikirarin dakatar da shi.

Kara karanta wannan

A Karon Farko, Kwankwaso Ya Yi Magana Mai Jan Hankali Bayan Dakatar da Shi a Jam'iyyar NNPP

NNPP.
Kwankwaso da shugabannin NNPP Hoto: SaifullahiHon
Asali: Twitter

NEC ta ce wasu ‘yan taware da su ka zauna, su na barazanar dakatarwa ko korar babban ‘dan siyasar su na batawa kan su lokaci ne a tafiyar NNPP.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Babu wata kungiya ko wasu daidaikun mutane da za su iya dakatar da tsohon ‘dan takaran shugaban kasar daga NNPP, wannan shi ne ra’ayin NEC.

Kamar yadda aka rahoto Mallam Kawu Ali ya na fada, zargin Kwankwaso da yin zama da Bola Tinubu, Atiku Abubakar ko Peter Obi abin darayi ne.

Jam’iyyar ta ce a duk lokacin da za ayi taro irin wannan, Kwankwaso ya na sanar da shugabanninsa.

Ba a san da zaman BOT a NNPP ba

Shugaban NNPP na kasa, Mallam Kawu Ali ya shaidawa manema labarai a sakariyar NNPP da ke Abuja cewa ba a bi ka’ida wajen kafa majalisar BOT ba.

Kara karanta wannan

Buba Galadima Ya Tona Asiri Kan Abin Da NNPP Ta Yi Kafin Kwankwaso Ya Gana Da Tinubu, Bayanai Sun Fito

Wannan majalisar amintattu a karkashin jagorancin Dr. Boniface Aniebonam ne ta ke da’awar dakatar da Kwankwaso daga NNPP na tsawon watanni shida.

Kawu Ali ya yi wannan bayani bayan ya hadu da ‘yan majalisarsa ta NWC da kuma shugabannin NNPP daga jihohi 36 da ke tare da tsohon gwamnan Kano.

Babban mai binciken kudi kuma kakakin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa, Ladipo Johnson ya karanto jawabin shugaban jam’iyyar.

A wurin ne Ladipo Johnson ya tabbatar da cewa mutanen Agbo Major ‘yan taware ne a jam'iyyar da kwanan nan wasu 'ya 'yanta su ke sauya-sheka.

Rikicin gwamnoni da mataimakansu

A tarihin Najeriya ku na da labari an yi wasu Gwamnonin jihohi da su ka yaki mataimakansu a lokacin da ake kan mulki, har da Abdullahi Ganduje.

Abdullahi Ganduje ya yi fada da mataimakansa a zaman da su ka yi tare tsakanin 2015 da 2018, akasin irin yadda ya yi wa Rabiu Kwankwaso biyayya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng