Jam'iyyar PDP a Jihar Zamfara Ta Zargi APC Da Kokarin Kawo Rudani a Jihar
- Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Zamfara, ta bankaɗo wani tuggu da jam'iyyar APC ke shiryawa a jihar
- Jam'iyyar PDP ta yi zargin cewa jam'iyyar APC na ƙoƙarin ganin mulkin jihar ya gagareta gudanarwa
- Jam'iyyar ta hannun shugabanta ta kuma zargi tsohon gwamnan jihar Abdulaziz Yari, da yunƙurin ba ƴan majalisar dokokin jihar cin hanci domin su tsige Dauda Lawal
Jihar Zamfara - Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Zamfara ta koka kan shirin ba ƴan majalisar dokokin jihar cin hanci domin su tsige gwamna Dauda Lawal.
Jam'iyyar ta kuma caccaki shirin da jam'iyyar All Progressives Congress (APC) take yi a jihar na ƙoƙarin ganin ta samu fifiko a kan shari'ar gwamnan jihar wacce har yanzu ba a faɗi sakamakonta ba, cewar rahoton Nigerian Tribune.
A yayin ganawa da manema labarai a birnin Gusau ranar Talata, muƙaddashin shugaban jam'iyyar na jihar, Mukhtar Muhammad Lugga, ya bayyana cewa jam'iyyar APC na ƙoƙarin ganin ta sanya mulkin jihar ya yi wa PDP wahala.
PDP ta aike da sabon zargi kan APC
Muƙaddashin shugaban ya yi zargin cewa jam'iyyar APC tana yi wa PDP sharri sannan ba ta son zaman lafiya ya ɗore a jihar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A kalamansa:
"A wata hira da aka yi ta yaɗawa, wani ɗan a mutun jam'iyyar APC, Mal Anas Anka, manajan gidan talbijin na Thunder Blowers, ya bayyana yadda tsohon gwamnan jihar Abdulaziz Yari ya ba shi kwangila."
"A cikin sautin muryar da aka naɗa, an jiyo Anka yana zargin cewa an ba alƙalai kuɗi domin su yi hakuncin da zai yi wa jam'iyyar APC daɗi a ƙarar zaɓen gwamnan jiha."
Lugga ya bayyana cewa tsohon gwamnan jihar, Sanata Abdulaziz Yari yana shirin ba ƴan majalisun dokokin jihar cin hanci domin su fara shirye-shiryen tsige gwamna Dauda Lawal.
NNPP Ta Musanta Dakatar Da Kwankwaso
A wani labarin kuma, shugaban jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) na jihar Kano, ya musanta cewa jam'iyyar ta dakatar da Rabiu Musa Kwankwaso.
Hashima Dunguruwa ya bayyana cewa har yanzu jam'iyyar tana tare da madugun ƴan Ƙwankwasiyya.
Asali: Legit.ng