Jihar Edo: Obaseki Ya Kori Hadiman Mataimakin Gwamna Shaibu

Jihar Edo: Obaseki Ya Kori Hadiman Mataimakin Gwamna Shaibu

  • Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya kori hadiman midiya na ofishin mataimakinsa, Philip Shaibu kan rashin ɗa'ar da suka nuna
  • Obaseki ya umarci mataimakin gwamna da ya riƙa miƙa bukatarsa ga ma'aikatar sadarwa da wayar da kan jama'a
  • Gwamnan ya kuma koka kan halayyar da hadiman midiyan suka nuna a wurin taro inda ake zargin sun yi kokarin shiga ta dole

Edo state - Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya kori baki ɗaya tawagar hadiman midiya masu aiki a ofishin mataimakin gwamna, Philip Shaibu.

Kwamishinan sadarwa da wayar da kan al'umma na jihar Edo, Chris Nehikhare, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar da yammacin ranar Litinin, 28 ga watan Agusta, 2023.

Gwamna Obaseki tare da mataimakinsa.
Jihar Edo: Obaseki Ya Kori Hadiman Mataimakin Gwamna Shaibu Hoto: Godwin Obaseki
Asali: Twitter

Ya ce daga yanzu ma'aikatar sadarwa da wayar kan al'umma zata riƙa kula da harkokin midiya na ofishin mataimakin gwamnan, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Zaftare Yawan Jami'an Gwamnati Masu Fita Kasar Waje Saboda Rage Kashe Kudi

A sanarwan, kwamishinan ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Gwamnatin jihar Edo ta kori hadiman midiya da ke ofishin mataimakin gwamna, tare da umarnin mataimakin gwamnan da ya nemi ma’aikatar sadarwa da wayar da kan jama’a kan ayyukan midiya na ofishinsa."

Obaseki ya bayyana cewa gwamnati ta ɗauki wannan matakin ne sakamakon abun takaicin da ya faru a wurin taron da ya gudana a Sir Victor Uwaifo Creative Hub' da ke Benin, babban birnin Edo.

Babban abinda ya sa aka kori hadiman

Gwamnatin Obaseki ta zargi tawagar midiya da koƙarin kutsa kai ta tsiya wajen shiga ɗakin taron, inda ta ƙara da cewa a daidai lokacin gwamna Obaseki da sauran manyan baƙi suna zaune a ciki.

Obaseki, gwamnan jam’iyyar PDP, ya ce abinda ma'aikatan midiya na Shaibu suka aikata a wurin ya saba wa ka’idojin da aka tsara na yadda harkokin midiya zasu gudana a wurin taron.

Kara karanta wannan

Ana Cacar Baki Tsakanin Ministan Tinubu Da Gwamnan PDP, Kwanaki 7 Da Shiga Ofis

Nehikhare ya bayyana nadamarsa kan yadda mataimakin gwamnan ya fice daga taron a ranar Litinin, kamar yadda Tribune Online ta rahoto.

An tattaro cewa Shaibu ya fice daga taron ne bayan da aka hana masu taimaka masa kan harkokin yada labarai shiga wajen taron.

Shekara 2 Abiodun Yana Rike Kuɗin Kananan Hukumom, Ciyaman Ga Osoba

A wani rahoton na daban Shugaban ƙaramar hukumar Ijebu ta gabas ya kai ƙorafin gwamnan Ogun ga tsohon gwamna, Aremo Olusegun Osoba.

Mista Adedayo, tsohon gogaggen ɗan jarida ya roƙi tsohon gwamnan, Mista Osoba, ya gaggauta sa baki a lamarin domin Abiodun ya sakar wa kananan hukumomi mara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262