Tinubu: Ba Da Jimawa Ba Za a Bayyana Obi a Matsayin Shugaban Kasa, Abure

Tinubu: Ba Da Jimawa Ba Za a Bayyana Obi a Matsayin Shugaban Kasa, Abure

  • Julius Abure ya bayyana wanda yake da tabbacin zai samu nasara a Kotun sauraron ƙorafin zaben shugaban ƙasa
  • Shugaban LP na ƙasa ya ce Peter Obi na dab da ɗarewa kujera lamba ɗaya a Najeriya da zaran Kotu ta yanke hukunci
  • Ya ce tun da jam'iyyar LP ta tsayar da Obi a babban zabe, baki ɗaya siyasar Najeriya ta canza salo

United States - Shugaban jam'iyyar Labour Party na ƙasa (LP), Julius Abure, ya ce ba da daɗewa ba Kotun sauraron ƙararrakin zabe zata ayyana Peter Obi a matsayin shugaban ƙasa.

Mista Abure ya yi wannan furucin ne yayin da yake jawabi ga wasu 'yan Najeriya da ke zaune a ƙasar Amurka a wata ziyara da ya kai ƙasar, kamar yadda The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Abba Vs Gawuna: Siyasa Ta Ƙara Ɗaukar Zafi a Kano, APC Ta Ɓullo da Sabuwar Dabarar Nasara a Kotu

Shugaban Labour Party na kasa, Julius Abure.
Tinubu: Ba Da Jimawa Ba Za a Bayyana Obi a Matsayin Shugaban Kasa, Abure Hoto: thecable
Asali: UGC

Obi, wanda ya zo na uku a sakamakon zaben shugaban ƙasan da aka gudanar a watan Fabrairu tare da jam'iyyarsa LP sun kalubalanci zaɓen a gaban Kotu.

Sun roƙi kotun sauraron kararrakin zabe da ta soke nasarar Bola Ahmed Tinubu, ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyar APC mai mulki.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yaushe Kotun zata yanke hukunci?

Shugaban LP na ƙasa, wanda ya kai ziyara ƙasashen Amurka da Burtaniya, ya ce suna tsammanin Ƙotun PEPT zata yanke hukunci gabanin ko ranar 16 ga watan Satumba, 2023.

Jaridar Independent ta tattaro Abure na cewa:

"Biyo bayan fafatawar da Peter Obi ya yi a babban zaben 2023, mun sauya aƙalar siyasar Najeriya, mun sa su gudun bala'i duk da kiɗinsu."
"Sun daina barci kwata-kwata, ba za su ƙara yin barci ba. Sun sace abin da ba nasu ba kuma ba za su yi barci ba sai mun kwato haƙƙinmu duka."

Kara karanta wannan

Daga Karshe An Bayyana Abin Da Ya Haifar Da Tsadar Rayuwa a Najeriya

"Muna sa ran za a yanke hukunci daga nan zuwa ranar 16 ga Satumba, 2023. Kuma ina a tabbacin Peter Obi zai zama shugaban kasa."
“Kada mu karaya, kada mu cire rai. Har yanzu dai muna sa ran samun nasara kuma ina da yakinin cewa Peter Obi zai karɓi ragamar mulkin Najeriya."

Mataimakin Gwamnan PDP Ya Fusata, Ya Fice Daga Wurin Taro

A wani rahoton kuma Mataimakin gwamnan Edo ya fice daga wurin taro a fusace bayan wulaƙancin da aka masa ranar Litinin.

An ga mataimakin gwamna wanda alamu suka nuna ƙarara bai ji daɗin abinda ya faru ba, ya jagoranci mukarrabansa suka fito daga wurin kana suka hau motocinsu suka ƙara gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel