Ogun: Shekara 2 Abiodun Yana Rike Kuɗin Kananan Hukumom, Ciyaman Ga Osoba

Ogun: Shekara 2 Abiodun Yana Rike Kuɗin Kananan Hukumom, Ciyaman Ga Osoba

  • Shugaban ƙaramar hukumar Ijebu ta gabas ya kai ƙorafin gwamnan Ogun ga tsohon gwamna, Aremo Olusegun Osoba
  • A wata wasiƙa da ya rubuta, Wale Adedayo ya ce shekara 2 kenan gwamnan yana riƙe kason tarayya na kananan hukumomi
  • Ya roƙi Mista Osoba ya shiga tsakani domin a riƙa sakar wa ciyamomi kuɗaɗensu na tarayya

Ogun state - Shugaban ƙaramar hukumar Ijebu ta gabas a jihar Ogun da ke Kudu maso Yammacin Najeriya ya rubuta doguwar wasiƙar ƙorafi zuwa ga tsohon gwamnan jihar, Aremo Olusegun Osoba.

A wasiƙar wacce ya rattaba adireshin Mista Osoba ranar Lahadi, 27 ga watan Agusta, Ciyaman ɗin Ijebu ta gabas, Wale Adedayo, ya yi korafin cewa gwamna Dapo Abiodun na riƙe haƙƙin kananan hukumomi.

Gwamna Dapo Aboidun na jihar Ogun.
Ogun: Shekara 2 Abiodun Yana Rike Kuɗin Kananan Hukumom, Ciyaman Ga Osoba Hoto: Prince Dapo Abiodun
Asali: UGC

Ciyaman ɗin ya zargi gwamna Abiodun da turmushe kason kuɗin kananan hukumomin da gwamnatin tarayya take turo wa duk wata na tsawon shekaru biyu da suka wuce.

Kara karanta wannan

Hadimin Atiku Ya Fadi Iya Wa'adin Da Ya Ragewa Bola Tinubu a Kan Kujerar Shugabanci, Ya Ba Shi Shawara

Jaridar Daily Trust ta rahoton Mista Adedayo na cewa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Tun lokacin da muka hau karagar mulki (Ciyamomin kananan hukumomi a jihar Ogun) a shekarar 2021, har yanzu ko kwandala daga cikin kason mu na FG ba ta iso gare mu ba."

Wakilin jaridar ya samu kwafin wasikar da shugaban ƙaramar hukumar Ijebu ta gabas ya rubuta wa tsohon gwamnan ranar Litinin, kuma Adedayo ya tabbatar da ita yayin da aka tuntuɓe shi.

Mista Adedayo, tsohon gogaggen ɗan jarida ya roƙi tsohon gwamnan, Mista Osoba, ya gaggauta sa baki a lamarin domin Abiodun ya sakar wa kananan hukumomi mara.

Ciyaman din ya roƙi Osoba ya sanya baki kuma ya yi wa gwamna magana domin ya bari, "Kason kuɗin kananan hukumomin da FG ke turo wa ya riƙa isa ga kowane ciyaman."

Kara karanta wannan

"Ya Kamata 'Yan Najeriya Su Shiga Ruɗani" Atiku Ya Ƙara Bankaɗo Abinda Tinubu Ya Yi a 1999 da 2023

Yaushe gwamnan ya fara rike kuɗin kananan hukumomin?

Shugaban karamar hukumar ya kuma yi zargin cewa an fara hana kananan hukumomi kason su na tarayya a jihar tun lokacin mulkin tsohon Gwamna, Sanata Ibikunle Amosun.

PM News ta rahoto Ciyamn din na cewa:

“Kamar yadda yake faruwa a yau, lamarin ya samo asali ne daga wani yunƙuri na taimaka wa wasu ƙananan hukumomi, waɗanda ba za su iya cika aikinsu ga jama’a ba saboda rashin kuɗi.”

Abba Vs Gawuna: Jam'iyyar APC Ta Roki Magoya Baya Su Dauki Azumi

A wani labarin kuma Siyasa ta ƙara zafi tsakanin jam'iyyar APC da NNPP mai mulkin Kano yayin da ake dakon hukuncin Kotu kan zaɓen gwamna.

Jam'iyyar APC ta buƙaci 'ya'yanta su tashi da azumi kana su dage da rokon Allah ya ba su nasara a Kotun zaɓe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel