Kotun Zabe Ta Tanadi Hukuncinta Kan Shari'ar Zaben Gwamnan Jihar Sokoto

Kotun Zabe Ta Tanadi Hukuncinta Kan Shari'ar Zaben Gwamnan Jihar Sokoto

  • Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Sokoto ta tanadi hukuncinta kan ƙarar da aka shigar da gwamnan jihar Ahmed Aliyu da mataimakinsa Idris Gobir
  • Kotun mai alƙalai uku ƙarƙashin jagorancin mai shari'a Haruna Mshelia ta sanar da hakan a ranar Asabar, 26 ga watan Agusta
  • Ɗan takarar jam'iyyar PDP, Saidu Umar, ya shigar da ƙara a kan Aliyu bisa zargin rashin cancanta da magudin zaɓe

Jihar Sokoto - Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Sokoto ta tanadi hukuncinta kan ƙarar da aka shigar da gwamna Ahmed Aliyu da mataimakinsa Idris Gobir, na jam'iyyar All Progressive Congress (APC).

Kotun mai alƙalai uku a ƙarƙashin jagorancin mai shari'a Haruna Mshelia, a ranar Asabar, 26 ga watan Agusta, ta bayyana cewa za ta sanarwa da ɓangarorin biyu ranar da za ta sanar da hukuncinta a cikin watan Satumba. cewar rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Atiku vs Tinubu: Jigon APC Ya Yi Hasashen Hukuncin Da Kotu Za Ta Yanke

Kotun zabe ta tanadi hukunci kan karar zaben gwamnan Sokoto
PDP na karar Ahmed Aliyu da mataimakinsa kan rashin cacanta da magudin zabe Hoto: redit:Office of the Press Secretary, Government House Sokoto
Asali: Facebook

Kotu ta tanadi hukunci kan gwamnan Sokoto

Sa’idu Umar na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya shigar da ƙara kan gwamna Aliyu bisa rashin cancanta da yin maguɗin zaɓe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lauyan Umar, Aare Olumuyiwa Akinboro, SAN, ya bayyana cewa akwai bambanci a tsakanin takardun kammala sakandire da da na jami'a na gwamnan da waɗanda hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta gabatar.

Akinboro ya kuma ƙara da cewa babu wata hukumar gwamnati da take da bayani akan akwai wata makarantar “Model Primary School”, wacce Gobir ya yi iƙirarin cewa ta ba shi satifiket ɗin kammala firamare, rahoton Tribune ya tabbatar.

Babban lauyan ya kuma yi nuni da cewa Aliyu da mataimakinsa sun kasa kare kansu inda suka gabatar da shaidu biyu kacal waɗanda suka kasa yin jayayya ko rushe abinda shaidun PDP 32 suka gabatar tare da tarin hujjoji.

Kara karanta wannan

Sabon Rikici: Dakarun 'Yan Sanda Sun Mamaye Babbar Sakatariyar APC Ta Ƙasa, Bayanai Sun Fito

Ya buƙaci kotun da ta soke zaɓen gwamna sannan ta bayyana Umar a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar na ranar 18 ga watan Maris.

Ministar Tinubu Ka Iya Rasa Mukaminta

A wani labarin kuma, hukumar ƴan yi wa ƙasa hidima (NYSC), ta yi magana kan taƙaddamar rashin kammala bautar ƙasa na ministar fasaha, al'adu da tattalin arziƙin fikira.

Hukumar ta tabbatar da cewa Hannatu Musa Musawa yanzu take yin bautar ƙasa wanda hakan ya saɓa doka, inda ta tabbatar cewa za ta ɗauki mataki a kai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng