Imo: Na Cika Alkawarin da Na Ɗauka Harda Kari, Gwamna Uzodinma
- Gwamnan Imo ya bayyana cewa ya cika dukkan alkawurran da ya ɗaukar wa ma'aikata harda karin wasu a zangonsa na farko
- Hope Uzodinma, shugaban kungiyar gwamnonin APC ya ce gwamnatinsa zata ci gaba da inganta walwala da jin daɗin ma'aikata
- A ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023 za a gudanar da zaben gwamnan Imo kuma Uzodinma na neman tazarce a inuwar APC
Imo state - Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma ya jaddada kudirin gwamnatinsa na ci gaba da inganta hukumar kula da ma’aikata ta jihar Imo da kuma sadaukarwa ga walwalar ma’aikata.
Da yake tsokaci kan kyakkyawan shugabanci, Gwamnan ya bayyana wasu daga cikin nasarorin da gwamnatinsa ta samu a ɓangaren ma'aikatan gwamnati.
Daga cikin ayyukan da ya yi, Uzodinma ya ambato gyaran Sakatariyar jiha, jigilar ma'aikata kyauta lokacin zuwa da komowa gida, kiwon lafiya kyauta da sauransu.
Uzodinma ya ce gwamnatinsa ta cika wa ma'aijata alƙawurran da ta ɗauka harda ɗori, kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A kalamansa gwamna Uzodinma ya ce:
"Ina so ku sani cewa ina daraja gudunmawarku da sadaukarwar ku. Gwagwarmayar ku da jajircewarku na da muhimmanci wajen ciyar gwamnati da jiharmu zuwa gaba."
"Ina tabbatar muku da cewa babu wani ma’aikacin gwamnati da za a ci mutuncin sa saboda ya sauke nauyinsa na zabe. Mu ci gaba da hada kai don gina jihar Imo mai karfi da wadata."
Ya kuma bada tabbacin jajircewa wajen magance matsalolin tsaro a jihar da ke da nasaba da siyasa domin ta haka ne kaɗai zai tabbatar da tsaro da jin dadin dukkan mazauna jihar.
Uzodinma ya yi wannan kalamai ne sa'ilin da ma'aikata suka kai masa ziyara cikin murna da farin ciki bisa aiwatar da tsarin ƙara girma da sauransu, The Cable ta tattaro.
Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un, An Tsinci Gawar Shugabar Alkalai a Yanayi Mara Kyau a Jihar Arewa
Shugaban ma’aikata, Barista Raymond Ucheoma ya yabawa gwamnan kan dimbin ayyukan da ya yi wa ma’aikatan da har yanzu ba a kwatanta su da sauran gwamnatocin baya ba.
Matatan Man Patakwal Zata Dawo Aiki a Watan Disamba, Ministan Tinubu
A.wani rahoton kun ji cewa Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta jaddata burinta na daina shigo da man fetur zuwa gida Najeriya nan da yan shekaru.
Ƙaramin ministan albarkatun fetur (Mai), Heineken Lokpobiri, ya ce a ƙarshen shekarar nan matatar Patakwal zata ci gaba da aiki.
Asali: Legit.ng