Rikicin Cikin Gida Zai Tarwatsa NNPP, An Kori Wanda Ya Kafa Jam’iyya Tun 2002

Rikicin Cikin Gida Zai Tarwatsa NNPP, An Kori Wanda Ya Kafa Jam’iyya Tun 2002

  • Watanni da nada shugaban rikon kwarya, an dakatar da Boniface Okechukwu Aniebonam daga NNPP
  • Mallam Abba Kawu Alli ya ce za a ladabtar da shugaban BOT da sakataren yada labarai na jam’iyya
  • Dr. Aniebonam shi ne wanda ya kafa jam’iyyar da ta ba Rabiu Kwankwaso damar takarar shugaban kasa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Rigimar da ake fama da ita a NNPP ta rikida sakamakon dakatar da shi kan shi wanda ya kafa jam’iyyar Dr. Boniface Okechukwu Aniebonam.

Rahoton Vanguard ya tabbatar da cewa shugaban jam’iyyar NNPP na kasa, Mallam Abba Kawu Alli ya dakatar da Dr. Boniface Okechukwu Aniebonam.

Baya ga Boniface Aniebonam, jam’iyyar ta ce an dakatar da sakataren yada labarai, Dr Agbo Major.

NNPP.
Magoya bayan NNPP Hoto: @KwankwasoRM
Asali: Twitter

NNPP: Matsayar Shugaban rikon kwarya

Shugaban NNPP na rikon kwarya, Mallam Abba Kawu Alli ya bayyana haka da yake karanto wani jawabi wanda shi da Oladipo Johnson su ka sa hannu.

Kara karanta wannan

Tsohon Hadimin Buhari Ya Yabawa Kokarin Gwamna Abba Gida Gida a Jihar Kano

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sanarwar ta ce an dakatar da wadannan shugabanni biyu ne har sai an ji makomar wani bincke na musamman da kwamitin da aka kafa ya ke gudanarwa.

Mista Oladipo Johnson shi ne mai binciken harkar kudi a jam’iyyar hamayyar ta NNPP na kasa. Leadership ta fitar da labarin rikicin cikin gidan a yau.

Rahoto ya zo cewa kafin a je ko ina sai aka ji Agbo Major wanda shi ne mai magana da yawun jam’iyyar ya na cewa babu wanda ya dakatar da su a NNPP.

A cewar Major, shi da shugaban majalisar amintattu watau Dr Boniface Okechukwu Aniebonam, su na nan a jam’iyyar da aka sani da alaman kayan marmari.

Wasan Nollywood ko Hollywood a NNPP

Sakataren yada labaran ya misalta abin da Kawu Alli ya yi da wasan Nollywood ko Hollywood kwanaki bayan yin barazanar korar 'dan takaran 2023.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu Ya Sa Labule da Rabiu Kwankwaso, Sun yi Kus-Kus a Aso Rock

Shi dai sabon shugaban jam’iyyar da ya shiga ofis bayan zaben 2023, ya ce Dr Boniface Aniebonam ya rika warware matakan da NWC ta dauka.

Wannan zargi ya jawo aka kafa kwamiti ya yi bincike a kan su kamar yadda doka ta yi tanadi ga masu shirya zagon kasa ko neman kunyata jam’iyya.

Silar rikicin NNPP bayan zabe

A watan Yuli, 2023 aka samu labari Kakakin NNPP na kasa, Dr. Agbo Major ya bayyana cewa NWC ta dakatar da shugabanninta da ke jihohi 7.

Major ya ce jam'iyyar ta daga wa jihohin Imo da Oyo kafa sakamakon zaben gwamna da na kananan hukumomi da ke tafe, hakan ya hargitsa jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng