Bola Tinubu Ya Sake Kebewa, Ya Sa Labule da Rabiu Kwankwaso a Fadar Aso Rock
- Rabiu Musa Kwankwaso ya kuma sa labule da Shugaban Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
- Wannan ne karo na biyu da fitaccen ‘dan siyasar ya hadu da shugaban kasar a cikin watanni biyu
- Bayan zaman da jigon NNPP ya yi da Atiku Abubakar, sai ga shi tare da Bola Tinubu a Aso Rock
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abuja - Jagoran jam’iyyar NNPP na kasa, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi wata ganawa da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Kamar yadda hadimin tsohon gwamnan ya bayyana a dandalin X, ‘yan siyasar sun hadu ne a yammacin ranar Alhamis.
Kusan babu wani cikakken bayani da ya fito a game da zaman Bola Ahmed Tinubu da Rabiu Kwankwaso har zuwa yanzu.
Hoton Kwankwaso a Aso Rock
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A sanarwar da Saifullahi Hassan ya fitar cikin daren yau a shafukansa, ya ce tattaunawar ta shafi harkokin kishin kasa ne.
Zuwa yanzu da mu ke tattara wannan rahoto, Madugun darikar siyasar ta Kwankwasiyya bai yi karin haske a shafinsa ba.
Haka zalika Mai girma shugaban Najeriya da hadiminsa ba su yi bayani kan wannan zama da shi ne na biyu a cikin kwanaki 85 ba.
Sanarwar Hadimin Kwankwaso
"A yau jagoran jam’iyyar New Nigeria People’s Party, @OfficialNNPPng na kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso @KwankwasoRM PhD FNSE, (24 ga watan Augusta, 2023), ya hadu da shugaban tarayyar Najeriya, a kan abubuwan da su ka shafi kasa."
Saifullahi Hassan Hadimin yada labarai ga Kwankwaso.
Kwankwaso ya zauna da Tinubu da Atiku
A cewar @babarh_, wani masoyin tsohon Gwamnan na Kano, Shugaban Najeriyan ne ya nemi ya yi zama da gwaninsu a birnin Abuja.
Ziyarar Kwankwaso zuwa fadar Aso Rock ta zo ne kwanaki kadan bayan ‘dan takaran PDP a 2023, Atiku Abubakar ya gana da shi.
Abdul Sageer sai dai ya ce: “Madugu”
“Jagoran gobe idan Allah ya so” Inji Umar Farouk Injay
@norrdeen3 ya rubuta: “Madugu Uban Talakawa”
Sani Haruna, Shamsu Salisu da Saifullahi Usman sai dai Hamdala, su ka ce: “Ma shaa Allahu”
Shi kuma wani mai suna Abubakar Sadiq Bichi, abin da ya dame shi dabam, cewa yake yi: “Gaskiya Tinubu na bukatar tela, wannan zulumbuwa har ina!”
Ministoci za su ci biliyoyi
Kun ji labari an rantsar da ministoci ba tare da mabiya Kwankwaso ko jam'iyyarsa ta NNPP sun iya samu wani mukami ba.
Kamar yadda Hukumar RMFAC ta yanka albashi, minista ya na samun N650,135.99, su 45 za su ci N6.9bn a shekaru hudu.
Asali: Legit.ng