Jami'ar Chicago Ta Amince Za Ta Saki Takardun Karatun Shugaba Tinubu
- Wa'adin mulkin Shugaba Tinubu ka iya zuwa ƙarshe ba shiri yayin da jami'ar jihar Chicago ta amince ta ba kotu takardun karatunsa
- Sai dai, jami'ar ta bayyana cewa za ta yi hakan ne a lokacin da ta kammala fahimtar abin da ke tsakanin Tinubu da Atiku Abubakar
- Amma jami'ar ta jihar Chicago ta tabbatar da cewa Shugaba Tinubu ya kammala karatunsa a jami'ar inda raba gardama kan taƙaddamar da ake gameda karatunsa
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Chicago, USA - Ta iya yiwuwa kwanakin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, a matsayin shugaban ƙasa sun kusa zuwa ƙarshe, yayin da jami'ar Chicago ta amince ta bayyana takardun karatunsa lokacin da yake ɗalibi a jami'ar.
Jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), a cikin wani rubutu da ta yi a Twitter ranar Alhamis, 24 ga watan Agusta, ta yi iƙirarin cewa jami'ar ta amince ta ba kotu takardun karatun Shugaba Tinubu.
Idan za a iya tunawa dai jam'iyyar PDP da ɗan takarar shugaban ƙasanta a zaɓen shugaban ƙasa na ranar 25 ga watan Fabrairu, ta nemi wata kotu a Amurka da ta tilasta jami'ar ta bayyana takardun karatun Shugaba Tinubu lokacin da yake ɗalibi a cikinta.
Sai dai, a cikin takardar da PDP ta sanya a Twitter, jami'ar ta tsaya akan matsayarta ta farko cewa Shugaba Tinubu ya kammala karatunsa a jami'ar sannan ba ta da wata masaniya kan ƙararrakin da ake yi wa shugaban ƙasar dangane da takardun karatunsa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Jam'iyyar PDP ta yi martani
Sanarwar na cewa:
"Yanzu ya tabbata a hukumance. Jami'ar Chicago a ƙasar Amurka a dalilin ƙarar da @OfficialPDPNig da ɗan takarar shugaban ƙasarta a zaɓen ranar 25 ga watan Fabrairu, @Atiku, ta amince ta saki takardun karatun Bola A. Tinubu."
"Akwai Babbar Matsala" Fitaccen Malami Ya Bayyana Hukuncin da Kotu Zata Yanke Kan Nasarar Tinubu a 2023
"Ƴan Najeriya da sauran mutanen ƙasashen waje sun ƙosa wannan bayanin ya fito domin zai taka rawar gani sosai wajen yanke hukuncin da kotu za ta yi kan ƙarar da ke a gabanta."
PDP Ta Dakatar Da Shugaban Matasa
A wani labarin kuma, jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta dakatarda shugaban matasan jam'iyyar na jihar Kwara.
Jam'iyyar ta dakatar da Halliru Dantsoho Mahmoud ne bisa wasu kalamai da ga yi akan tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki.
Asali: Legit.ng