Gwamna Ya Tura Sunayen Kwamisihinoni, ‘Yan Majalisa Sun Ki Karbar Mutane 17

Gwamna Ya Tura Sunayen Kwamisihinoni, ‘Yan Majalisa Sun Ki Karbar Mutane 17

  • An tantance wadanda Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya bada sunayensu domin zama Kwamishinoni
  • ‘Yan majalisar dokokin Legas sun amince da mutane 22 ne, amma mutane fiye da 15 ba su samu shiga ba
  • Zuwa yanzu ba a ji dalilin kin yarda da ragowar ba, majalisar ba za ta sake zama ba sai a makon gobe

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Lagos - Majalisar dokokin jihar Legas ta yi fatali da wasu daga cikin mutanen da Gwamna Babajide Sanwo-Olu yake so su zama kwamishinoni.

The Cable ta kawo rahoto cewa a jerin mutane 39 da Mai girma Babajide Sanwo-Olu ya ba majalisa sunayensu, 22 ne kadai aka yi amincewa da su.

Tun kafin a ki karbar ragowar mutane 17 da aka bada, wasu su ka rika yin korafi, ana zargin gwamnatin Legas da rashin adalci a raron mukaman.

Kara karanta wannan

Jerin Sunayen Ministocin Shari'a da Antoni Janar Na Tarayya da Aka Yi a Najeriya Tun Daga 1999

Gwamnan APC
Gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu ya zabi Kwamishinoni Hoto: @jidesanwoolu
Asali: Twitter

Kwamishinonin da aka tantance:

1. Misis Folashade Adefisayo

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

2. Farfesa. Akin Abayomi

3. Mista Yomi Oluyomi

4. Misis Folashade Ambrose

5. Miss Barakat Bakare

6. Mista Gbenga Omotosho

7. Injiniya Olalere Odusote;

8. Dr. Rotimi Fashola

9. Misis Bolaji Cecilia Dada

10. Mista Sam Egube;

11. Mista Olalekan Fatodu

12. Misis Solape Hammond

13. Mista Mosopefolu George

14. Injiniya Aramide Adeyoye

15. Mista Seun Osiyemi

16. Mr Rotimi Ogunwuyi

17. Dr. Olumide Oluyinka

Hon. Mudashiru Obasa ya jagoranci Majalisa

Rahoton da Vanguard ta fitar a yammacin Laraba ya ce Rt. Hon. Mudashiru Obasa ya jagoranci zaman majalisar dokokin da aka yi a garin Ikeja.

A cewar Mudashiru Obasa, kwamitin da ya yi wannan aiki ya bi tsauraran matakai wajen tantance wadanda za su rike kujerar kwamishononin.

Shugaban majalisar ya ce shugaban masu tsawatarwa, Hon. Fatai Mojeed mai wakiltar Ibeju-Lekki tun a 2015 yake jagorantar kwamitin.

Kwamishononin da aka amince:

1. Layode Ibrahim

2. Mista Mobolaji Ogunlende

Kara karanta wannan

Cacar Kujera: Sanatoci da ‘Yan Majalisa 3 da Aka Nada Ministocin Tarayya a Yau

3. Dr. Dolapo Fasawe

4. Bola Olumegbon

5. Mista Idris Aregbe

6. Miss Abisola Ruth Olusanya

7. Mista Moruf Akinderu Fatai

8. Mista Kayode Bolaji-Roberts

9. Injiniya Abiola Olowu

10. Misis Toke Benson-Awoyinka

11. Dr. Oreoluwa Finnih- Awokoya

12. Mista Yakub Adedayo Alebiosu

13. Mista Lawal Pedro SAN

14. Mista Tunbosun Alake

15. Mista Gbenga Oyerinde

16. Dr. Adekunle Olayinka

17. Dr. Jide Babatunde

18. Mista Afolabi Ayantayo

19. Mista Tokunbo Wahab

20. Mista Olakunle Otimi-Akodu

21. Mista Jamiu Alli-Balogun

22. Mista Abdulkabir Ogungbo

Game da wadanda aka amince a rantsar da su, majalisar dokokin ta tuna masu gwamnatin Legas da mutanen su ka zo yi wa aiki ba daidaiku ba.

Rahoto ya ce sai ranar 28 ga Agustan nan ‘yan majalisar dokokin jihar za su sake zama

Majalisar jihar Kaduna

A Kaduna an taba ji majalisar dokoki ta ki yarda wani ya zama kwamishina, laifinsa shi ya rika cin mutuncin Nasir El-Rufai wanda yake gwamnan jihar.

A 2022 ne Yusuf Tanimu Zailani ya zama sabon shugaban majalisar, ya na mai canzar Aminu Abdullahi Shagali wanda ya yi murabus da hannunsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng