Ministocin da Shugaba Tinubu Ya Nada Sun Yi Kadan a Najeriya Inji Jigon APC

Ministocin da Shugaba Tinubu Ya Nada Sun Yi Kadan a Najeriya Inji Jigon APC

  • Mamban kwamitin APC na miƙa mulkin shugaban kasa ya ce ministocin da shugaba Bola Tinubu ya naɗa sun yi kaɗan a Najeriya
  • Aliyu Audu ya bayyana cewa akwai buƙatar a ƙara matsar da harkokin shugabanci zuwa kusa da jama'a
  • Sai dai da aka tambaye shi adadin yawan ministocin da ya kamata, jigon jam'iyya mai mulkin ya ce ba zai iya faɗin adadi ba

Abuja - Mamban jam'iyyar APC mai mulki kuma babban jigo, Aliyu Audu, ya bayyana cewa adadin ministocin da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya naɗa sun yi kaɗan.

Wannan kalamai na Mista Audu na zuwa ne yayin da ke cece kuce da sukar da ake yi kan cewa shugaba Tinubu ya naɗa ministoci har guda 45.

Jigon APC, Aliyu Audu da Bola Tinubu.
Ministocin da Shugaba Tinubu Ya Nada Sun Kadan a Najeriya Inji Jigon APC Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Yayin wata hira a Channels tv cikin shirin Sunrise Daily, Mista Audu, mamban kwamitin miƙa mulkin shugaban ƙasa na APC, ya ce:

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Bayyana Yadda Zai Mu'amalanci Ministocinsa Kan Ayyukan Da Ya Ba Su

"Ba na tunanin ministoci 45 sun isa, haka ba na jin 48 sun isa. Idan kuka duba muna da mutane sama da miliyan 200 a ƙasar nan. Ga shi Muna cikin rikici."

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Adadin ministoci nawa ya kamata Tinubu ya naɗa?

Da aka tambaye shi ya ba da adadin ministocin da ya ke so a naɗa, jigon APCn ya amsa da cewa, "Ba zan iya faɗin adadi ba."

Yayin da yake tofa albarkacin bakinsa kan batun, jigon jam’iyyar APC ya bayyana cewa shugaba Tinubu, tsohon gwamnan Legas na ganin ya kamata shugabanci ya ƙara matsa wa kusa da jama'a.

A rahoton Vanguard, Jigon APC ya ƙara da cewa:

“Mutane da yawa sun dauka ya wuce gona da iri amma dubi yadda Legas ta koma cikin shekaru 24 da yadda sauran jihohi suka koma cikin shekaru 24."

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Shugaba Tinubu Ya Aike Da Sabon Gargadi Ga Wike Da Sauran Ministocinsa

"Ba wai ina magana kan yuwuwa ko yanayin yadda jihar take bane a wancan lokacin, ina nufin yadda ta bunƙasa tun daga wancan lokacin zuwa yanzu."

Gwamnatin Tinubu Zata Gina Gada a Babban Titin Abuja Zuwa Lokoja

A wani rahoton na daban kuma tsohon gwamnan Ebonyi kuma ministan ayyuka, David Umahi, ya ce FG zata gina gadar sama a titin Abuja-Lokoja.

Mista Umahi ya ce gwamnatin Bola Tinubu zata gina wannan gada ne a matsayin hanya ɗaya ta warware yawan ambaliyar ruwan da ke yawan aukuwa a kan titin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262