Nyesom Wike: Sabon Minista Ya Yi Alkawarin Cusawa Ma’aikata Cutar Hawan Jini
- Nyesom Wike ya wayi gari a matsayin ministan Abuja, ya nanata cewa ba wasa ya zo yi a birnin ba
- Sabon ministan tarayyar ya fadawa ma’aikatan da ba su da niyyar aiki a Abuja su canza ma’aikata
- Wike ya bada umarnin tsabtace Abuja, ya na ma iyi wa shugaban AEPB alkawarin tashin hawan jini
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abuja - Ganin yadda abubuwa su ka tabarbare a babban birnin tarayya na Abuja, Nyesom Wike ya zaburar da ma’aikatansa da su zabura.
Vanguard ta rahoto Nyesom Wike ya na gargadin ma’aikatan birnin tarayya da su ka kara kaimi ko kuwa su nemi canjin wani wurin aiki.
A nan ne sabon ministan ya umarci shugaban hukumar AEPB mai kula da tsabtar Abuja da ya tabbata ya yi kokari wajen gusar da kazanta.
'Wahala za ta zo da hawan jini'
Wike wanda ya ce zai dawo da martabar garin Abuja yake cewa zai taso shugaban na AEPB a gaba, har sai ta kai ya jawo jinin shi ya tashi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A bangaren sufuri kuwa, rahoton ya ce ministan ya fadawa ma’aikatan da ya samu a sakatariyar cewa wahala ta gan su da zuwansa Abuja.
Wike wanda ya yi magana da Ingilishin Pidgin, ya karbi takardu a hannun babban sakatare na ma’aikatar tarayya a FCTA, Olusade Adesola.
Wike: "Za a ga ayyuka a kan ayyuka"
Zan tabbata cewa Abuja ta samu mafi kyau. Za ku ga ayyuka a kan ayyuka, kuma ayyukan da za a kammala, ba a wadanda za a watsar ba.
Ba na cikin masu watsi da ayyuka. Ina fara aiki ne idan akwai kudi, saboda haka za mu duba asusunmu kafin mu fara wata kwangila.
Nayi imani da manufar shugaba Bola Tinubu, kuma kafin a kai ko ina, jama’a za su ga bambanci.”
- Nyesom Wike
Kamar yadda aka samu labari daga Nairaland, tsohon gwamnan na Ribas ya bukaci darektan da ke kula da fitulu a kan titi da ya haskaka Abuja.
A bangaren ta, karamar minista, Dr Mariya Mahmoud ta ce Wike zai maiamaita abin da ya yi a Ribas inda ya shafe shekaru takwas a jere a mulki.
Samuel Ortom ya yabi Wike, Utsev
Samuel Ortom ya na cikin ‘Yan tawagar G5 da su ka ki goyon bayan Atiku Abubakar a zaben 2023, ya yabi wasu ministocin da Bola Tinubu ya nada.
Tsohon Gwamnan ya jinginar da adawa ya na yabon Joseph Utsev da Nyesom Wike, ya ce za su yi abin a yaba bayan zamansu ministocin tarayya.
Asali: Legit.ng