Nyesom Wike Ya Ce Bai Karbi Muƙamin Minista Domin Daga Tutar Jam'iyyar APC Ko Ta PDP Ba

Nyesom Wike Ya Ce Bai Karbi Muƙamin Minista Domin Daga Tutar Jam'iyyar APC Ko Ta PDP Ba

Sabon ministan FCT, Nysome Wike, ya bayyana tsare-tsarensa a kan mazauna birnin Abuja

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wike ya bayyana cewa ba ya zo Abuja domin daga tutar jam'iyyar APC ko ta PDP ba ne, ya zo ne ya aiwatar da gyare-gyare

Tsohon gwamnan na Ribas ya ce ya karɓi muƙamin ne domin taimakawa Tinubu cika alƙawuransa

FCT, Abuja - Sabon ministan Babban Birnin Tarayya (FCT) Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana cewa bai zo Abuja domin ɗaga tutar jam'iyyar APC ko ta jam'iyyar PDP ba.

Ya ce ya zo Abuja ne domin tabbatar da cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu, ya samu damar cika alƙawuran da ya yi wa mutanen garin yayin yaƙin neman zaɓe.

Wike ya fadi abinda ya kawo shi Birnin Tarayya Abuja
Nyesom Wike ya ce bai karɓi muƙamin minista domin daga tutar APC ko PDP ba. Hoto: Nyesom Ezenwo Wike
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Sabon Ministan Shugaba Tinubu Ya Ce Zai Yi Aiki Kamar Magini a Yayin Da Ya Shiga Ofis

Wike ya ce bai zo Abuja domin ɗaga tutar APC ko PDP ba

Nyesom Wike ya yi jawabin ne ga manema labarai, jim kaɗan bayan karɓar rantsuwar fara aiki kamar yadda @DejiAdesogan ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Wike ya ce ba wai ɗaga tutar jam'iyya Abuja ke buƙata ba a yanzu, inda ya bayyana cewa zai iya kafe tutocin APC, PDP har ma da ta jam'iyyar Labour a ofishinsa.

Ya ce babban burinsa shi ne ya ga ya inganta tsare-tsaren da birnin na tarayya ke da shi ta fuskar gine-gine da sauran bangarori daban-daban na Abuja.

Nyesom Wike dai na cikin ministoci 45 da shugaba Bola Tinubu ya rantsar domin fara aiki a ranar Litinin ɗin da ta gabata kamar yadda ta ruwaito.

Wike zai fatattaki 'yan acaba makiyaya daga Abuja

A baya Legit.ng ta kawo rahoto kan bayanin da sabon ministan Birnin Tarayya Abuja Nyesom Wike ya yi, na cewa zai fatattaki 'yan acaba da makiyaya daga cikin ƙwaryar birnin.

Kara karanta wannan

Wike Ya Bayyana Abin Da Shugabannin PDP Suka Fada Masa Kan Nadin Da Tinubu Ya Masa

Wike ya ce ba zai ƙyale shanu su ci gaba da shigowa cikin birnin na Abuja ba, inda ya ce zai tattauna da makiyaya da sauran masu ruwa da tsaki a kan hakan.

Haka nan Wike ya sha alwashin yin iyakance inda 'yan acaba da masu napep za su iya zuwa a cikin birnin, tare da yin garambawul kan kasuwannin da ake da su a Abuja.

Wike ya ce sai da ya tuntubi PDP kafin karɓar muƙamin Tinubu

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan martanin da Nyesom Wike ya yi wa masu sukarsa kan karɓar muƙamin minista da ya yi a gwamnatin Tinubu.

Ya ce sai dai ya tuntuɓi duk wasu masu ruwa da tsaki na jam'iyyar PDP gabanin ya amince da tayin muƙamin ministan da Tinubu ya yi ma sa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng