Shehu Sani Ya Yi Magana Kan Batun Hadewar Jam'iyyun PDP da LP
- Ƴan takarar jam'iyyu 18 ne suka fafata a lokacin zaɓen shugaban ƙasan Najeriya na watan Fabrairun 2023
- Hukumar zaɓe ta INEC ta bayyana ɗan takarar jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Tinubu, a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen
- Yanzu an fara raɗe-raɗin jam'iyyun da suka zo na biyu da na uku a zaɓen, Peoples Democratic Party (PDP), Labour Party (LP) da wasu jam'iyyun na shirin haɗewa
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja - Akwai raɗe-raɗin cewa jam'iyyun adawa da ke Najeriya na shirin haɗewa waje ɗaya domin tunkarar zaɓukan da ke tafe nan gaba a ƙasar nan.
Jam'iyyar Labour Party (LP), ta Peter Obi, wacce ta yi suna sosai, inda a ke raɗe-raɗin cewa tana shirin haɗewa da babbar jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP).
Wannan haɗewar da a ke raɗe-raɗin jam'iyyun za su yi, za su yi ta ne domin ƙwace mulki a hannun jam'iyyar All Progressives Congress (APC).
Batun haɗewar LP, PDP: Shehu Sani ya yi martani
Da yake martani kan raɗe-raɗin, Shehu Sani, tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, ya bayyan lamarin a matsayin "abu mai kyau ga dimokuraɗiyya."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Jigon na jam'iyyar PDP ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na Twitter, a ranar Litinin, 21 ga watan Agustan 2023.
"Raɗe-raɗin cewa jam'iyyun adawa na shirye-shiryen haɗewa, abu ne mai kyau ga dimokuraɗiyya. Yanzu sun koma karatun ilmin labarin ƙasa bayan an yi girgizar ƙasa."
Kafin zaɓen shugaban ƙasa na watan Fabrairu, wasu daga cikin jam'iyyun adawa sun yi ƙoƙarin yin haɗaka, amma hakan bai yiwu ba.
An Bukaci Akpabio Ya Yi Murabus
A wani labarin kuma, an buƙaci shugaban majalisar dattawa na cigaba da shan matsin lamba kan sai ya yi murabus.
Wata ƙungiyar mata ta buƙaci Sanata Godswill Akpabio, ya gaggauta yin murabus daga shugabancin majalisar dattawa, bisa tarihin cin hanci da rashawa da yake da shi a baya.
Asali: Legit.ng