Mai Ba Da Shawara Kan Makabartu, Wurin Ninkaya Da Sauran Mukamai Na Daban Da Gwamnoni Su Ka Bayar
Ba tun yau ba, gwamnonin jihohi su ka fara kirkirar ma'aikatu ko kuma masu ba su shawara na musamman da ba a saba ganin irin su ba
Jihar Osun - Gwamna Ademola Adeleke ya yi martani kan nada Alhaji Oyetunji Abefe a matsayin mai ba da shawara kan wurin ninkaya a gidan gwamnati.
Adeleke ya ce mukamin na nan fiye da shekaru 12 a jihar da gwamnatin APC ta kirkira, Legit.ng ta tattaro.

Source: Facebook
Meye Adeleke ya ce kan mukamin?
Gwamnan yace ba kamar yadda mutane ke tunani ba, mukamin ba shi da alaka da wurin ninkaya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kakakin gwamnan, Olawale Rasheed a cikin wata sanarwa ya ce mukamin ya shafi harkar sufuri ne, cewar BBC.
Ya ce:
"Ya ce bangaren ya shafi motoci da direbobi a gidan gwamnati wanda ya fi shekaru 12.
"Mai ba da shawara na musamman a wannan harkar shi ne ya ke kula da bangaren."
Mukamai na daban da sauran gwamnoni su ka bayar.
1. Mai ba da shawara a kan zaurawa
Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya nada Balaraba Ibrahim don kula da zaurawa da taimakonsu.
2. Mai ba da shawara a kan harkokin makabartu
A 2018, tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya nada Yakubu Nagoda a matsayin mai ba da shawara na musamman a kan makabartu.
3. Mai ba da shawara a kan wutar kan tituna
Har ila yau, Abdullahi Umar Ganduje a 2020 ya nada masu ba shi shawara guda uku a kan kula da wutar titunan birnin.
4. Ma'aikatar Farin Ciki
A 2017, tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha ya kirkiri ma'aikata ta musamman don jin dadin jama'a.
Okorocha ya nada Ogechi Ololodi a matsayin kwamishina a ma'aikatar.
Musulmai Sun Karyata Cewa An Nuna Musu Wariya A Osun
A wani labarin, Kungiyar Musulmai ta jihar Osun ta karyata jita-jitar cewa gwamna jihar, Ademola Adeleke ya nuna wariya a mukaman gwamnatinsa ga Musulmai.
Shugaban kungiyar, Sheikh Mustapha Olayiwola shi ya bayyana haka ga 'yan jaridu inda ya ce sun gamsu da wannan gwamnati ta Gwamna Ademola a jihar.
Ana zargin gwamnan da nuna wariya a wasu mukaman gwamnatinsa musamman ga Musulmai a jihar.
Asali: Legit.ng

