Bola Tinubu: An Shiga Tashin Hankali Yayin Da Aka Bayyana 'Yan Hana Ruwa Gudu a Aso Rock

Bola Tinubu: An Shiga Tashin Hankali Yayin Da Aka Bayyana 'Yan Hana Ruwa Gudu a Aso Rock

  • Primate Elijah Ayodele na cocin INRI Evangelical Spiritual Church ya yi hasashen ɓullowar wasu sabbin ƴan hana ruwa gudu a Villa
  • A cewar Ayodele, sabbin ƴan hana ruwa gudun za su wahalar da Shugaba Tinubu sannan za su iya ɓata gwamnatinsa saboda muradinsu
  • Faston ya yi nuni da cewa wasu daga cikin sabbin ministocin Tinubu za su zama cikin ƴan hana ruwa gudun kuma duk sun fito ne daga yankin Kudu maso Yamma

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Ikeja, jihar Legas - Ana ta shiga cikin halin rashin tabbas yayin da Primate Elijah Ayodele, babban faston cocin INRI Evangelical Spiritual Church, ya bayyana ɓullar wasu sabbin ƴan hana ruwa gudu da za su wahalar da Shugaba Tinubu.

A cikin wani sabon bidiyo da ya saki a shafinsa na Twitter a ranar 18 ga watan Agusta, faston ya bayyana cewa ƴan hana ruwa gudun za su fito ne a yankin Kudu maso Yamma, kuma za su wahalar da Shugaba Tinubu da gwamnatinsa.

Kara karanta wannan

Masanin Tattalin Arziƙi Ya Fadi Abinda Zai Faru Idan Ministocin Tinubu Suka Fara Aiki

Ayodele ya bayyana yan hana ruwa gudu a Villa
Primate Ayodele ya hango yan hana ruwa gudu a Aso Rock Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Waɗanda za su zama ƴan hana ruwa gudu a Aso Rock

Ayodele ya bayyana cewa waɗanda za su zama ƴan hana ruwa gudun na hannun daman shugaban ƙasar ne, kuma za su ja masa abin da bai taɓa tunani ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewar Ayodele, wasu daga cikin ƴan hana ruwa gudun sun haɗa da sabbin ministoci, kuma duk sun fito ne daga yankin Kudu maso Yamma na ƙasar nan

Ya ƙara da cewa shugaban ƙasar yana ɓuƙatar addu'a sannan fadar shugaban ƙasar tana buƙatar a tsarkake ta sannan ya buƙaci ƴan Najeriya da su cigaba da addu'a domin samun zaman lafiya a ƙasar nan.

An gargaɗi Tinubu kan maƙiya a Aso Rock

A jikin bidiyon faston ya rubuta cewa:

"Na ƙara hango ƴan hana ruwa gudu na tattaruwa akan gwamnatin @officialABAT. Fadar shugaban ƙasa yakamata ta sa ido sosai sannan ta cigaba da addu'ar samun sakamako mai kyau a gwamnatin nan."

Kara karanta wannan

Cire Tallafi: Babban Malamin Addini Ya Fadawa Tinubu Abinda Zai Faru Idan Bai Yi Maganin Halin Da Ake Ciki Ba

Primate Ayodele sananne wajen bayyana hasashensa akan Najeriya da shugabanci. Ya yi kalamai sosai akan zaɓen shugaban ƙasa na 2023, musamman akan tikitin Muslim-Muslim na jam'iyyar APC.

Ayodele Ya Gargadi Shugaba Tinubu

A wani labarin kuma, Primate Elijah Ayodele ya aike da muhimmin saƙo ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Babban faston ya gargaɗi shugaban ƙasar kan halin ƙuncin ɗa ake ciki a ƙasa, a dalilin tsare-tsaren da ya ɓullo da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng