Tsigaggen Surukin Kwankwaso Bai Yarda Ya Rasa Kujera Saboda Takardar Firamare ba

Tsigaggen Surukin Kwankwaso Bai Yarda Ya Rasa Kujera Saboda Takardar Firamare ba

  • Mukhtar Umar-Zakari zai je kotun daukaka kara saboda a rusa hukuncin tsige shi daga Majalisa
  • ‘Dan majalisar na Tarauni ya fitar da jawabi cewa ya na sa ran samun nasara a babban kotun kasar
  • Hon. Zakari ya ce bai yi karyar takardun karatu ba kamar yadda kotun karar zabe ta yi hukunci

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Kano - Muktar Umar-Zakari (NNPP-Kano) ya sha alwasin sake samun nasarar shari’a bayan da kotun sauraron karar zabe ta tunbuke shi.

Hukumar dillacin labarai ta ce Mukhtar Umar-Zakari wanda ya wakilci mazabar Tarauni a jihar Kano a majalisar tarayya ya fitar da jawabi.

Tsohon ‘dan majalisar da ya lashe zaben 2023 a karkashin jam’iyyar NNPP ya daukaka kara a kotun gaba domin ganin ya rike kujerarsa.

Surukin Kwankwaso
Rabiu Kwankwaso tare da 'Yan Majalisar Kano Hoto:Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Facebook

Hafizu Kawu ya doke NNPP

Mukhtar Umar-Zakari bai gamsu da hukuncin da aka yi ba inda alkalan kotun zabe su ka ba Hon. Hafizu Kawu damar ya karbe kujerar da yake kai.

Kara karanta wannan

Shari'ar Gwamnan Kano: Mataimakin Shugaban Majalisa Ya Roki Yan Najeriya Su Taya APC Addu'ar Samun Nasara Kan PDP

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hafizu Kawu wanda ya wakilci Tarauni a APC tsakanin 2019 da 2023 zai koma majalisar wakilai sakamakon hukuncin Mai shari’a I.P. Chima.

Leadership ta rahoto Umar-Zakari wanda bai dade da zuwa majalisa ba ya na cewa bai yi karyar takardun boko kamar yadda aka yanke hukunci ba.

Za a tafi kotun daukaka kara

‘Dan siyasar ya na mai biyayya ga doka, ya nuna zai sake shigar da kara a kotun daukaka kara domin kuwa ya yi canjin suna tun kafin zaben 2023.

An haife ni ne a Muktar Umar, na shiga makarantar firamaren Hausawa, na gama a matsayin Muktar Umar.
Kamar yadda yake a duka takardun firamare, sakandare da gaba da sakandare na domin a duba. Daga baya na kara Zakari a cikin sunana.
Bayan na bi duk ka’idojin tsarin mulkin kasa a kan canjin suna, na samu shaidar kotu da wallafar bugun canjin sunan daga jarida.

Kara karanta wannan

Muddin Aka Sake Kara Farashin Fetur, Za Mu Birkita Kasar Nan da Yajin Aiki Inji NLC

Ina fatan kotun daukaka kara za ta sauke nauyinta, ta sake duba shari’ar Alkalan kotun zabe domin a samu zaman lafiya da bin doka.
A matsayin mai bin doka da shari’a da dokar kasa, zan cigaba da neman gaskiya a babban kotu, in karbe kujerar da ‘yan Tarauni su ka zabe ni.

- Mukhtar Umar-Zakari

NNPP ta ci kujeru a Kano

Bayan zabe, kun samu labarin yadda Muhammad Bello Shehu ya doke Hon. Aminu Sulaiman Goro da Shuaibu Abubakar a mazabar Fagge a Kano.

APC ta zo ta uku a kujerar 'dan majalisa mai wakiltar Fagge sai dai APC ta rike kujerun yankunan Takai, Tudun Wada da Doguwa a zaben bana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel