Tinubu Ya Hana Kowa Kujerar Ministan Fetur, Ya Yi Koyi da Al’adar Buhari a Mulki
- Har Muhammadu Buhari ya sauka daga mulki, shi ya rike ma’aikatar harkokin man fetur na kasa
- Magajinsa Bola Ahmed Tinubu ya gaji wannan tsari, Heineken Lokpobiri zai zama karamin Minista
- A cikin Ministocin Tinubu babu soja, fararen hula ne za su jagoranci harkokin tsaro a Najeriya
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abuja - Kamar yadda Muhammadu Buhari ya yi a lokacin da ya ke ofis na tsawon shekaru takwas, Bola Ahmed Tinubu zai zama ministan fetur.
A jeringiyar mukaman da aka rabawa ministoci a yammacin Laraba, Legit.ng Hausa ta fahimci ba a warewa kowa kujerar ministan harkar fetur ba.
Kamar yadda magabacinsa ya yi a lokacin mulkinsa, Bola Tinubu ya zabi Heineken Lokpobiri ya zama karamin minista a ma’aikatar harkar man.
Mutumin Bayelsa zai sake zama Ministan fetur
‘Dan siyasar na jihar Bayelsa ya na cikin wadanda aka aika da sunansa zuwa majalisa daga baya, shi ba bakon zama a majalisar FEC ba ne.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Buhari ya fara nada Lokpobiri ya zama karamin minista a 2015. Daga baya Timipre Sylva daga Bayelsan, ya canji Ibe Kachikwu a ma'aikatar mai.
Kafin yanzu, ‘dan siyasar ya rike matsayin Sanata mai wakiltar yammacn Bayelsa, kuma ya je majalisar dokoki har ya zama shugabanta a 1999.
Ministan Neja Delta zai fito daga baya
Bayan haka, mun fahimci a ministocin da za a rantsar a ranar Litinin, babu wanda zai rike ma’aikatar harkar Neja-Delta da aka kirkira a 2008.
Da farko mun yi tunanin Nyesom Wike zai jagoranci ma’aikatar, sai ga shi an zabe shi ya zama Ministan birnin Abuja, abin da ba a saba gani ba.
'Dan Kudu zai zama Ministan Abuja
Tun daga Halliru Dantoro, ‘yan Arewa su ka saba zama Ministocin Abuja. Bola Tinubu ya sabawa wannan tsohuwar al’ada ta shekara da shekaru.
Nasir El-Rufai, Aliyu Moddibo Umar, Muhammad Adamu Aleiro, Bala Mohammed da Muhammad Musa Bello duk sun fito ne daga yankin Arewa.
Kafin nan an yi Mohammed Abba Gana da Ibrahim Bunu, Jeremiah Useni, Mamman Kontagora, Gado Nasko, Hamza Abdullahi da Mamman Vatsa.
Badaru a Ma'aikatar tsaro
Wani wuri da Tinubu ya saba shi ne dauko wadanda ba sojoji ba domin su jagoranci harkar tsaro. Cif Olusegun Obasanjo ne ya yi irin haka a 2003.
An ji Muhammad Badaru, ‘dan kasuwa wanda ya karanci ilmin akanta zai zama Ministan tsaro sai Bello Matawalle zai zama karamin minista.
Asali: Legit.ng