Jerin Sababbin Ministoci 45 Da Mukaman Da Shugaba Bola Tinubu Ya Rabawa Kowa
- An kirkiro sababbin ma’aikatun tarayya da Bola Tinubu ya rabawa duka Ministocinsa mukamai
- Za a rantsar da majalisar FEC babu Malam Nasir El-Rufai, Abubakar Sani Danladi da Stella Okotete
- Bello Matawalle zai zama karamin Ministan tsaro, Nyesom Wike zai kula da birnin tarayya Abuja
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abuja - Yanzu nan labari ya fito daga fadar shugaban Najeriya cewa Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya rabawa ministoci mukaman da za su rike.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Ajuri Ngelale, ya sanar da haka ga 'yan jarida a yammacin Laraba, za a rantsar da ministocin a ranar Litinin.
A rabon mukaman da aka yi, Nyesom Wike zai zama Ministan babban birnin tarayya Abuja, Ibrahim Geidam zai jagoranci ma'aikatar 'yan sanda.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ministoci da za su rike mukamai
- Hannatu Musawa – Ministar fasaha, al’adu da tattalin arzikin fikira
- Muhammad Badaru – Ministan tsaro
- Bello Matawalle - Karamin Ministan tsaro
- Yusuf T. Sunumu – Karamin Ministan ilmi
- Ahmed Dangiwa – Ministan gidaje da raya birane
- Abdullahi Gwarzo - Karamin gidaje da raya birane
- Atiku Bagudu – Ministan kasafi da tsara tattalin arziki
- Jihar Kaduna – Ministan muhalli
- Mariya Mahmud – Karamar Ministan Abuja
- Bello Goronyo - Karamin Ministan ruwa
- Abubakar Kyari – Ministan harkokin gona da abinci
- Tahir Mamman – Ministan ilmi
- Sa’idu Alkali – Ministan cikin gida
- Yusuf Tuggar – Ministan harkokin waje
- Ali Pate – Ministan lafiya da cigaban al’umma
- Ibrahim Gaidam – Ministan harkokin ‘yan sanda
- Maigari Ahmadu – Karamin Ministan karafa
- Shuaibu Audu – Ministan karafa
- Muhammed Idris – Ministan yada labarai da wayar da kai
- Lateef Fagbemi – AGF kuma Ministan shari’a
- Simon Lalong – Ministan kwadago
- Imman Suleiman Ibrahim – Karamar Ministar harkokin ‘yan sanda
- Zephianiah Jisalpo – Ministan harkoki na musamman
- Joseph Utsev – Ministan harkar ruwa
- Aliyu Sabi Abdullah – Karamin Ministan gona da abinci
- Festus Keyamo – Ministan harkokin jirgin sama
- Betta Edu - Ministar jin kai da yaki da talauci
- Heineken Lokpobiri – Karamin Ministan man fetur
- John Enoh – Ministan wasanni
- Nyesom Wike – Ministan birnin Abuja
- Bosun Tijjani – Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani
- Ishak Salako – Karamin Ministan muhalli
- Wale Edun – Ministan kudi da tattalin arziki
- Bunmi Tunji-Ojo – Ministan tattalin arzikin teku
- Adebayo Adelabu – Ministan makamashi
- Tunji Alausa – Karamin Ministan lafiya da kula da jama’a
- Dele Alake – Ministan ma’adanai
- Lola Ade-John – Ministan yawon bude ido
- Adegboyega Oyetola – Ministan sufuri
- Doris Anite – Ministar kasuwanci da hannun jari
- Uche Nnaji – Ministan kimiyya, fasaha da kirkire-kirkire
- Nkiruka Onyejeocha – Karamar Ministan kwadago da samar da ayyuka
- Uju Kennedy – Ministar harkokin mata
- David Umahi – Ministan ayyuka
- Ekperikpe Ekpo – Karamar Ministar gas
- Abubakar Momoh – Ministan matasa
Da Dumi-Dumi: Kamfanin NNPC Ya Karbo Bashin Dala Biliyan 3 Don Inganta Farashin Naira, An Fadi Yadda Za A Biya Kudin
An ga Atiku wajen Kwankwaso
Daga baya an ji yadda Rabiu Musa Kwankwaso ya karbi bakuncin Atiku Abubakar bayan an yi watsi da jam'iyyar NNPP wajen rabon mukamai.
Yayin da Abdullahi Ganduje ya hadu da Nyesom Wike, tsohon mataimakin shugaban Najeriya ya hadu da madugun Kwankwasiyya a gida a Abuja.
Asali: Legit.ng