Masanin Tattalin Arziƙi Ya Ce Da Zarar Ministocin Tinubu Sun Fara Aiki Abubuwa Za Su Daidaita

Masanin Tattalin Arziƙi Ya Ce Da Zarar Ministocin Tinubu Sun Fara Aiki Abubuwa Za Su Daidaita

  • Duk da halin matsin tattalin arziƙi da ake ciki, akwai 'yan Najeriya da ke yi wa gwamnatin Tinubu kyakkyawan zato
  • Babban malamin jami'a Dakta Adigun Muse, ya yi kira ga 'yan Najeriya da su ƙara haƙuri da gwamnatin Tinubu
  • Saƙon na sa yana zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da kokawa kan matsin da cire tallafin mai ya jefa 'yan ƙasa ciki

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Epe, jihar Legas - Dakta Adigun Muse, tsohon shugaban sashen ilimin kimiyyar siyasa na jami'ar jihar Legas (LASUED), ya bayyana cewa 'yan Najeriya za su ji daɗin tsarukan tattalin arziƙin da Tinubu ya zo da su a gaba.

Ya bayyana hakan ne ranar Laraba, 16 ga watan Agusta a yayin da yake zantawa da Legit.ng, inda ya jaddada cewa bayan wuya sai daɗi.

Kara karanta wannan

Cire Tallafi: Babban Malamin Addini Ya Fadawa Tinubu Abinda Zai Faru Idan Bai Yi Maganin Halin Da Ake Ciki Ba

An nemi 'yan Najeriya da su yi haƙuri da tsarukan Tinubu
Masanin tattalin arziƙi ya nemi 'yan Najeriya su yi haƙuri da tsare-tsaren Shugaba Tinubu. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

An nemi 'yan Najeriya su yi haƙuri da tsarukan Tinubu

Dakta Muse ya shaidawa Legit.ng cewa har yanzu ministocin Tinubu ba su fara aiki ba, inda ya ba da tabbacin cewa da sun fara aiki komai zai daidaita.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ƙara da cewa tuntuni dama 'yan Najeriya na fuskantar matsin tattalin arziƙi musamman ma batun karyewar darajar naira da ake samu.

Sai dai ya roƙi Shugaba Bola Tinubu da ya yi ƙoƙarin rage raɗaɗin talaucin da 'yan ƙasa ke ciki, saboda gudun kar a kai mutane bango.

Muse ya kuma yi kira ga 'yan siyasar Najeriya a kowane mataki da su yi ƙoƙarin rage almubazzaranci da dukiyar 'yan ƙasa.

An faɗawa Tinubu abinda zai faru idan aka ci gaba da shan wahala

A baya Legit.ng ta yi rahoto kan shawarar da babban Fasto Primate Elijah Ayodele, ya bai wa Shugaba Tinubu kan halin matsi da ake ciki.

Kara karanta wannan

Daga Karshe An Bayyana Dalilin Da Ya Sanya Jirgin Sojin Saman Najeriya Ya Yi Hatsari a Jihar Neja

Ya ce 'yan Najeriya za su yi ma sa bore idan aka ci gaba da tafiya a hali na matsin tattalin arziƙin da ake ciki.

Ya bayyana hakan ne ta hannun mai taimaka ma sa a kafafen sada zumunta Osho Oluwatosin kamar yadda jarida Nigerian Tribune ta wallafa.

Oshiomole ya koka kan yadda Tinubu ya samu tattalin arziƙin ƙasa

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan Allah wadai da yadda Shugaba Tinubu ya tsinci halin tattalin arziƙin Najeriya daga gwamnatin Buhari da Oshiomole ya yi.

Oshiomole wanda sanata ne da ke wakiltar Edo ta Arewa a Majalisar Dattawa, ya bayyana cewa ba za a iya shawo kan matsalar tattalin arziƙin Najeriya cikin gaggawa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng