An Bayyana Lokacin Shugaba Tinubu Zai Rantsar Da Wike, Badaru Da Sauran Ministocinsa

An Bayyana Lokacin Shugaba Tinubu Zai Rantsar Da Wike, Badaru Da Sauran Ministocinsa

  • Rahotanni sun nuna akwai yiwuwar shugaban ƙasa Bola Tinubuya rantsar da ministocinsa a ranar Litinin
  • Wani majiya a fadar shugaban ƙasa ya bayyana cewa ofisoshin shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin tarayya da na SGF sun fara shirye-shirye
  • Ana sa ran Shugaba Tinubu zai rantsar da ministoci 45 ciki har da tsaffin gwamnoni na jihohin Rivers da Osun, Nyesom Wike da Gboyega Oyetola

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola yana duba yiwuwar rantsar da majalisar ministocinsa a ranar Litinin, 21 ga watan Agusta, kusan wata uku bayan an rantsar da shi a kujerar shugabancin ƙasar nan.

A cewar rahoton The Guardian, wani majiya a fadar shugaban ƙasa ne ya bayyana hakan, inya ya ƙara da cewa Shugaba Tinubu na iya rantsar da ministocinsa 45 da majalisar dattawa ta amince da su.

Kara karanta wannan

Sojojin Juyin Mulkin Nijar Za Su Tuhumi Shugaba Bazoum, Sun Bayyana Dalilai

Shugaba Tinibu zai rantsar da ministoci
Shugaba Tinubu zai rantsar da ministocinsa ranar Litinin Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Jan ƙafar da shugaba Tinubu ya yi wajen zaɓo ministocinsa ya sanya wasu ƴan Najeriya sun fara dawowa daga rakiyar tafiyarsa, inda suka daina yabawa da kamun ludayin salon mulkinsa.

Shugaba Tinubu zai rantsar da ministoci ranar Litinin

Tun da farko akwai alamun cewa ministocin da majalisar dattawa ta tantance tare da amincewa da su, na iya fara aiki a ranar Laraba, 16 ga watan Agusta, tun da ita ce ranar da ake gudanar da taron majalisar zartaswa ta tarayya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Amma majiyar ya bayyana cewa Shugaban ƙasan bai sanya rantsar da ministoci ba a cikin jadawalin abubuwa da zai gudanar a wannan satin.

An kuma tattaro cewa ofisoshin sakataren gwamnatin tarayya da na shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa, suna ta gudanar da shirye-shiryen rantsar da ministocin a ranar Litinin.

A satin da ya gabata ne dai, majalisar dattawa ta amince da ministoci 45 daga cikin 48 da Shugaba Tinubu ya aike da sunayensu domin tantancewa da amincewa, su zama ministoci a gwamnatinsa.

Kara karanta wannan

"Abun Kunya": 'Yan Najeriya Sun Fusata Bayan Ganin Dakarun Tsaro Na Musamman Da Ke Gadin Seyi Tinubu

Shugaba Tinubu Ya Nada Sabon Babban Sakataren Fadar Shugaban Kasa

Ku na da labari shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa sabon babban sakataren fadar shugaban ƙasa.

Shugaban ƙasar ya nada Olufunso Adebiyi wanda ya fito daga jihar Ekiti a matsayin sabon babban sakataren, biyo bayan ritayar da magabacinsa ya yi daga kan muƙamin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel