Jigon PDP Osita Chidoka Ya Ce PDP Za Ta Iya Rushewa Idan Ba a Ɗauki Matakin Da Ya Dace Ba

Jigon PDP Osita Chidoka Ya Ce PDP Za Ta Iya Rushewa Idan Ba a Ɗauki Matakin Da Ya Dace Ba

  • Jigon jam'iyyar adawa ta PDP ya nemi a yi gyare-gyare a jam'iyyar domin gudun kar ta ruguje
  • Osita Chidoka, wanda tsohon ministan sufurin jiragen sama ne ya yi wannan kira a yayinda ake tattaunawa da shi a talabijin
  • Ya ce akwai abubuwa da dama da PDP ya kamata ta koya daga jam'iyyar Labour ta Peter Obi

Babban jigo a jam'iyyar PDP, ya ce jam'iyyar za ta iya rugujewa idan ba a ɗaukar ma ta matakai ba cikin gaggawa.

Ya ce mambobin jam'iyyar da dama sun koma jam'iyyar Labour a zaɓen da ya gabata.

Chidoka ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Channels ranar Laraba, 16 ga watan Agusta.

Jigon PDP ya nemi jam'iyyar ta ɗauki wasu sabbin matakai
Jigon PDP Osita Chidoka ya nemi a yi sauye-sauye ko jam'iyyar ta ruguje. Hoto: Osita Chidoka
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Muddin Aka Sake Kara Farashin Fetur, Za Mu Birkita Kasar Nan da Yajin Aiki Inji NLC

Chidoka ya fadi matakan da suka dace PDP ta ɗauka

Chidoka wanda tsohon ministan sufurin jiragen sama ne, ya ce kwanan nan jam'iyyar PDP za ta fara wallafa takardu na suka gwamnatin APC da Bola Tinubu ke jagoranta.

Ya ƙara da cewa PDP jam'iyya ce da ta shafe shekaru 16 tana mulki, sannan kuma ta shafe shekaru takwas tana adawa.

Ya kuma bayyana cewa akwai buƙatar jam'iyyar PDP ta yi wa kanta sabbin tsare-tsare domin yin adawa da jam'iyyar APC mai mulki yadda ya kamata.

Chidoka ya kuma ce idan PDP ba ta tashi tsaye ta yi abinda ya kamata ba, za a neme ta a rasa gaba ɗaya nan ba da jimawa ba.

Ya kamata PDP ta koyi darasi daga ƙananun jam'iyyu

Osita Chidoka ya kuma ce dole ne PDP ta koyi darussa daga sabbin ƙananun jam'iyyu, ta yadda suka lashe zaɓe a inda jam'iyyar ke da magoya baya.

Kara karanta wannan

Tsohon Abokin Tafiyar Buhari Ya Ambato Kuskuren Da Shugaba Tinubu Ya Fara Daga Hawa Mulki

Ya bayyana cewa akwai wurare da dama da jam'iyyar Labour da Peter Obi ke jagoranta ta lashe, waɗanda asalinsu na masoya jam'iyyar PDP ne a zaɓen 2023 da ya gabata.

Saboda haka ne Chidoka ya ga dacewar tashin jam'iyyar PDP wajen samun jajirtattun shugabanni da za su zo da sabbin sauye-sauyen da za su taimakawa jam'iyyar kamar yadda Vanguard ta wallafa.

Atiku ya ziyarci Kwankwaso watanni biyar bayan zaɓe

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan ziyarar da ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP Atiku Abubakar, ya kai wa takwaransa na jam'iyyar NNPP Rabiu Musa Kwankwaso.

Ziyarar dai na zuwa ne aƙalla watanni biyar bayan kammala zaɓen shugaban ƙasa na 2023 da ya gudana a watan Fabrairu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng