A Karshe, Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Shugaban Jam’iyyar Labour Party Na Kasa

A Karshe, Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Shugaban Jam’iyyar Labour Party Na Kasa

  • Kotun daukaka kara a garin Benin, babban birnin jihar Edo ta kawo karshen rikicin shugabanci a jam'iyyar Labour Party
  • Kotun ta tabbatar da Julius Abure a matsayin ainahin shugaban jam'iyyar na kasa, tana mai bayyana cewa mutum daya ba zai iya dakatar da shugaban ba
  • Obiora Ifoh, kakakin jam'iyyar ta Labour Party, ya bayyana cewa kotun ta yanke hukuncin ne a ranar Litinin

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Benin, Edo - Kotun daukaka kara da ke garin Benin, babban birnin jihar Edo ta tabbatar da cewar Barista Julius Abure shine dai shugaban jam'iyyar Labour Party (LP) na kasa.

A cewar jaridar The Sun, Obiora Ifoh, babban sakataren labaran jam'iyyar Labour Party na kasa ne ya bayyana ci gaban a cikin watan sanarwa da ya saki a ranar Litinin, 14 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan

Kyau Ya Hadu Da Kyau: Diyar Biloniya Indimi Ta Amarce Da Babban Dan Kasuwar Kasar Turkiyya

Julius Abure ne Jam'iyyar Labour Party na kasa
A Karshe, Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Shugaban Jam’iyyar Labour Party Na Kasa Hoto: The Labour Party
Asali: UGC

Kotun daukaka kara ta yi watsi da shari'ar da ake yi kan shugaban jam’iyyar Labour na kasa

A wani hukuncin bai daya da suka yanke, alkalai Theresa Ngolika Abadua, Fatima Akinbami da Sybil Nwaka-Gbagi sun yi watsi da daukaka karar a shari’ar Lucky Shaibu v. Julius Abure da 5 ORS (Daukaka kara mai lamba: CA/B/93/2023), rahoton Vanguard.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewar Ifoh, wani Lucky Shauibu da ya yi ikirarin shi mamban shugabancin Labour Party ne a gudunma ta 3 a karamar hukumar Esan ta arewa maso gabashin jihar Edo ya sanar da dakatar da Abure daga Labour Party.

Dalilin da yasa kotun daukaka kara ta ayyana Abure shugaban jam'iyyar Labour na kasa

A cewar hukuncin, hakan ya yi daidai da sashi na 13 da 17 na kundin tsarin mulkin jam’iyyar Labour Party, da kuma dokar zabe ta waje na 2022, musamman ma lokacin da jam’iyyar ta bayyana kotun daukaka kara a matsayin wanda ba a san ta ba.

Kara karanta wannan

Ahir dinku: Wani malamin addini ya fusata, ya gargadi Turawa kan tunzura yaki a Nijar

Ifoh ya ce:

“Kotun gaba daya ta soke dakatarwar da aka yi a baya da kuma duk wani mataki da aka dauka kan Kwamred Julius Abure ”

Kotu Zata Yanke Hukunci da Karar Da Peter Obi Ya Kalubalanci Nasarar Tinubu

A wani labarin, mun ji a baya cewa kotun sauraron ƙararrakin zaben shugaban kasa a Najeriya ta ƙarƙare sauraron karar da ɗan takarar shugaban ƙasa na Labour Party, Peter Obi, ya shigar gabanta.

An ahoto cewa Kotun mai zama a Abuja ta ce zata sanar da ranar yanke hukunci kan ƙarar da Obi da LP suka ƙalaubalanci nasarar shugaban ƙasa, Bola Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel