El-Rufai Ya Fice Zuwa Turai Bayan Ajiye Ƙudurin Zama Ministan Tinubu
- Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya fice zuwa ƙasar waje
- Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da batun ƙin tabbatar da shi matsayin minista a gwamnatin Tinubu
- El-Rufai ya sanar da haƙura da muƙamin ministan, sannan ya ba da sunan wanda zai maye gurbinsa
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya fice zuwa ƙasar waje jim kaɗan bayan sanar da haƙura da ƙudurin zama minista a gwamnatin Tinubu da ya yi.
An bayyana cewa El-Rufai zai tafi Turai ne, amma zai fara biyawa ta ƙasar Egypt kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Majalisa ta ƙi tabbatar da El-Rufai matsayin minista
A makon da ya gabata ne dai Majalisar Dattawan Najeriya ta ƙi tabbatar da El-Rufai da wasu mutane biyu matsayin ministoci a gwamnatin Tinubu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
El-Rufai da Stella Okotete daga jihar Delta da kuma Danladi Abubakar da ya fito daga jihar Taraba ne majalisar ta ƙi tabbatarwa saboda dalilai na tsaro.
Wani sanatan jihar Kogi mai suna Sanata Sunday Karimi ne ya fara ƙalubalantar El-Rufai a zauren Majalisar Dattawa a lokacin da ya zo domin tantance shi.
El-Rufai ya gana da Shugaba Tinubu a ranar Talata
Biyo bayan ƙin tabbatar da shi da majalisar ta yi, Nasir El-Rufai ya gana da Shugaba Bola Tinubu a fadar gwamnatin Tarayya a ranar Talata.
Duk da dai ba a bayyana takamaiman abinda suka tattauna ba, wata majiya ta shaidawa jaridar Premium Times cewa El-Rufai ya faɗawa Tinubu cewa baya sha'awar zama ministan, amma zai riƙa ba da shawara matsayinsa na ɗan ƙasa.
Majiyar ta ce El-Rufai ya shaidawa Tinubu cewa zai tafi ƙasar Netherlands domin ci gaba da karatun digirinsa na uku.
An kuma bayyana cewa El-Rufai ya ba da shawarar a maye gurbinsa da Jafaru Ibrahim Sani matsayin minista daga jihar Kaduna.
Majalisa ta miƙawa Tinubu sunayen ministoci 45 da ta tabbatar
Legit.ng a baya ta yi rahoto kan sunayen mutane 45 da Majalisar Dattawa ta miƙawa Shugaba Tinubu a matsayin waɗanda ta tabbatar domin su zama ministoci.
Mai taimakawa Tinubu kan harkokin Majalisar Dattawa, Abdullahi Gumel ne ya bayyana hakan a zantawarsa da manema labarai.
Asali: Legit.ng