WAIWAYE: ‘Na Fi So Na Ba Tinubu Gudunmawa Daga Waje’, El-Rufai Ya Magantu Kan Mukamin Minista

WAIWAYE: ‘Na Fi So Na Ba Tinubu Gudunmawa Daga Waje’, El-Rufai Ya Magantu Kan Mukamin Minista

  • Rashin tabbatar da Mallam Nasir El-Rufai a matsayin minista na ci gaba da haddasa cece-kuce a soshiyal midiya
  • Wasu rahotanni sun kawo cewa El-Rufai ya daina sha'awar minista a gwamnatin Bola Tinubu, wasu rahotanni kuma sun ce 'cabals' ne suka hana tabbatar da shi
  • Sai dai tsohon gwamnan jihar Kadunan a cikin wani tsohon bidiyo da ke yawo a intanet ya ce ya fi so ya ba Tinubu gudunmawa a matsayin daga waje maimakon aiki a matsayin minista

Wani tsohon bidiyo na tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai yana bayyana matsayinsa dangane da samun mukami a gwamnatin Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana.

A tuna cewa tsohon gwamnan na cikin zababbun gwamnonin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da suka tsaya tsayin daka kuma suka marawa Tinubu baya har ya zama shugaban kasa.

Kara karanta wannan

El-Rufai Ya Bada Sunan Wanda Zai Canje Shi, Ya Cire Sha’awar Zama Ministan Tinubu

El-Rufai ya ce ya fi so ya ba Tinubu gudunmawa a matsayin dan waje
WAIWAYE: ‘Na Fi So Na Ba Tinubu Gudunmawa Daga Waje’, El-Rufai Ya Magantu Kan Mukamin Minista Hoto: Nasir El-Rufai
Asali: Facebook

Burina bayan mika mulki, El-Rufai

Sai dai kuma El-rufai, a wata hira da aka yi da shi kafin ya mika mulki ga magajinsa, Uba Sani a jihar Kaduna, ya bayyana matsayinsa kan mukamin minista a gwamnatin Tinubu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A hirar da aka yi a gidansa, da jaridar Premium Times, El-Rufai ya bayyana cewa ya fi so ya yi aiki a wajen gwamnatin Tinubu sannan ya bayyanawa Tinubu gaskiyar da wasu ba za su iya fada masa ba idan bukatar hakan ya taso.

El-Rufai ya ce:

"Na kasance minista shekaru 20 da suka wuce. Na samu damar zama ministan babban birnin tarayya shekaru 20 da suka wuce. Darakta Janar na BPE na shekaru hudu, kuma zan cika shekaru 63 nan da mako guda daya yau.
"Kuma magana ta gaskiya, na yarda cewa Najeriya na da tarin matasa masu hazaka da za su iya yin duk wani aiki da za a basu. Kuma ina da tarin wadannan matasa, da yawa da na yi aiki da su, da dama da na horar da su tsawon shekaru.

Kara karanta wannan

Ministocin Tinubu: Tsohon Na Hannun Daman Peter Obi Ya Roki Majalisa Ta Tantance El-Rufai

"Kuma na fada ma Asiwaju sau da dama cewa da wuya ace akwai aikin da za ka bani da ba zan iya samo maka wani matashi da zai yi shi fiye da ni ba.
"Shakka babu, bai yarda da wannan ba, abu ne da ake kan tattaunawa.
"Abun da na fi so bayan na mika mulki da yardar Allah shine na dauki hutu sannan na kammala Ph.D dina a bangaren shugabanci da manufofin gwamnati a wata jami'a da ke Neterlands.
"Bayan cika wa'adin mulkina, ina niyan kammala Ph.D na, na rubuta takardata, sannan na kula da yarana daga nan zan yanke shawara kan abu na gaba.
"Shakka babu, zan so jam'iyyarmu ta yi nasara. Zan kasance a kasa kuma ina nan don ba Asiwaju Bola Tinubu gudunmawa domin ya zama shugaban kasa mai nasara a duk bangaren da zan iya; amma zan fi son haka a matsayin mai ba da shawara daga waje wanda zai iya fada masa abun da sauran mutane ba za su fada masa ba."

Kara karanta wannan

Nadin Ministoci: Almajiran Sheikh Dahiru Bauchi Na So Tinubu Ya Cire El-Rufai Cikin Ministocinsa, Sun Fadi Dalili

El-Rufai ya daina sha'awar zama minista

A wani labarin kuma, mun ji cewa Nasir El-Rufai bai sha’awar zama minista a sabuwar gwamnatin tarayya.

Nasir El-Rufai bai sha’awar yin aiki da Bola Ahmed Tinubu bayan abin da ya faru a wajen tantance wadanda ake so su zama ministoci a kasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng