Jam'iyyar NNPP Ta Ja Kunnen Shugaban Jam'iyyar APC Na Kasa, Abdullahi Ganduje
- Shugabannin jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) sun aike da muhimmin gargaɗi zuwa ga Abdullahi Umar Ganduje
- Shugabannin sun gargaɗi shugaban jam'iyyar APC na ƙasa da ya kiyayi shuga harkar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso
- Shugabannin na NNPP sun yi nuni ds cewa Rabiu Kwankwaso ba tsaran Abdullahi Ganduje ba ne a siyasance
FCT, Abuja - Shugabannin jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) sun aike da saƙon gargaɗi ga sabon shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje.
Shugabannin sun gargaɗi Ganduje da ya fita harkar ɗan takarar shugaban ƙasan ta a zaɓen ranar 25 ga watan Fabrairun 2023, Rabiu Musa Kwankwaso, rahoton Daily Trust ya tabbatar.
Ganduje a cikin ƴan kwanakin nan ya yi kira ga Kwankwaso da ya dawo jam'iyyar APC tun da yanzu shi ne shugaban jam'iyyar na ƙasa.
Amma da yake tattaunawa da manema labarai bayan gudanar da taron kwamitin gudanarwar jam'iyyar na ƙasa (NWC), a birnin tarayya Abuja, shugaban jam'iyyar NNPP na ƙasa, Abba Kawu Ali, ya bayyana cewa sun yi mamakin zaɓar Ganduje da APC ta yi.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Abba Kawu Ali ya bayyana cewa abun akwai mamaki yadda APC ta zaɓi Ganduje a matsayin shugabanta duk kuwa da tarin badaƙalolin da suka baibaye shi.
Shin Kwankwaso tsaran Ganduje ne?
Ya bayyana cewa babu yadda za a yi a riƙa haɗa Kwankwaso da Ganduje, saboda Kwankwaso ya yi wa sabon shugaban na jam'iyyar APC fintinkau.
Haka zalika, mai binciken kuɗi na ƙasa na jam'iyyar NNPP, Ladipo Johnson, ya bayyana cewa Kwankwaso a ɓangaren siyasa ba tsaran Ganduje ba ne inda ya gargaɗe shi, da ya kiyayi yin irin waɗannan kalaman.
Dan Majalisa Ya Fadi Dalilin Da Ya Sa Hankalin PDP Ya Tashi Kan Zaman Ganduje Shugaban Jam'iyyar APC
Johnson ya bayyana cewa taron na sunna daga cikin ƙoƙarin gina jam'iyyar ta yadda za ta amfani ƴan Najeriya.
Ganduje Ya Kada Hantar PDP
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ɗan majalisar dokokin jihar Kano, ya yi wa jam'iyyar PDP a jihar Kano shaguɓe.
Yusuf Sulaiman ya bayyana cewa shugabancin jam'iyyar APC da Abdullahi Umar Ganduje ya samu, ya sanya hantar jam'iyyar PDP ta kaɗa.
Asali: Legit.ng