Cikakken Jerin Sunayen Shugabannin Kwamitocin Majalisar Dattawa
- Majalisar dattawan Najeriya ta tantance da tabbatar da ministoci 45 daga cikin 48 a ranar Litinin, 7 ga watan Agusta
- Majalisar dattawan ta bayyana cewa dalilai na tsaro ne ya hana ta tantance sauran ministoci uku
- Jim kadan bayan zaman na ranar Litinin, shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya sanar da sabbin kwamitoci da sanatocin da za su shugabance su
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abuja - Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya sanar da shugabannin kwamitocin majalisar dattawan a ranar Litinin, 7 ga watan Agusta.
Akpabio ya bayyana kwamitocin majalisar dattawa
Shugaban majalisar dattawan ya bayyana shugabannin kwamitocin majalisar bayan tabbatar da 45 daga cikin ministocin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu 48 a zaman majalisar na ranar, rahoton Vanguard.
Cikakkun sunayen kwamitocin da Akpabio ya sanar
Sanata Adams Oshiomhole, tsohon gwamnan jihar Sokoto Aminu Tambuwal da tsohon shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan na daga cikin wadanda za su shugabanci kwamitocin, rahoton NTA News.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sunaye da shugabannin kwamitocin
- Tsohon shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan (Tsaro)
- Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal (Gidaje)
- Tsohon gwamnan jihar Edo, Adams Oshiomhole (Harkokin cikin gida)
- Sen Godiya Akwashiki (Sojin sama)
- Buhari Abdul-Fata (Jiragen sama)
- Osita Izunaso (Kasuwannin Hadada-hadar kudi)
- Cyril Fasuyi (Ayyukan Gwamnati)
- Seriake Dickson (Sauyin yanayi)
- Jide Ipisagba (Harkokin Man fetur)
- Aliyu Wadada (Asusun gwamnati)
- Kaka Shehu Lawan (Ayyuka na musamman)
- Patrick Ndubueze (Ayyuka)
- Solomon Adeola (Kasafin kudi)
- Musa Sani (Kudi)
- Abiru Tokunbo (Bankuna)
- Isa Jubril (Kwastam)
- Elisha Abbo (Al'adu da yawon bude ido)
- Victor Umeh (Yan Najeriya da ke kasashen waje)
- Lawal Adamu Usman (Ilimi)
- Akintunde Yunus (Muhalli)
- Ibrahim Bomai (Birnin tarayya)
- Abubakar Sani Bello (Harkokin waje)
- Banigo Harry (Lafiya)
- Abubakar Yari, (Albarkatun ruwa)
- Enyinaya Abaribe (Wutar lantarki)
- Aliyu Wamakko (Basussukan gida da na waje)
- Adamu Aliero (Sufurin kasa)
- Daniel Olugbenga (Sojin ruwa)
- Barinada Mpigi (Niger Delta)
- Mohammed Monguno (Shari'a)
- Yemi Adaramodu (Matasa da wasanni)
- Ireti Kingigbe (Harkokin mata)
- Orji Kalu (Saida hannun Jari)
- Mustapha Sabiu (Noma)
- Aliyu Bilbis (Sadarwa)
- Asuquo Ekpenyong (NDDC)
- Idiat Oluranti (SDGs)
- Usaini Babangida (FERMA)
- Abdulaziz Yaradua (Sojin kasa)
- Yau Sahabi (Harkokin kasashen Nahiyar Afrika)
- Diket Plang (Daukar ma'aikata)
- Imaseun Neda (Korafe-korafen jama'a)
- Allwell Iheanacho (Harkokin gwamnati)
- Jarigbe Jarigbe (Gas)
- Etang Williams (Danyen mai)
- Sadik Umar (Kasuwanci da zuba jari
- Osita Ngu (Ma’adinai)
- Dandutse Muntari (Manyan Makarantun Kasa)
- Patrick Ifeanyi Ubah (Jihohi da Kananan Hukumomi)
- Abdulhamid Malam Madori (Harkokin yan sanda)
- Afolabi Salisu (Laifukan yanar gizo)
- Ali Sharafadeen (INEC)
- Fadahunsi Anthony (Masana’antu)
- Ahmed Ningi (Zama dan Kasa)
- Yahaya Abdul (Tsare-tsaren kasa)
- Umar Shehu (Tsaron kasa)
- Monday Ogberu (Sayen kayan gwamnati)
- Titus Zam (Tsari da kasuwanci)
- Eze Emeka (Yada labarai)
- Sunday Karimi (Ayyukan majalisa)
- Aminu Iya Abbas (Kimiyya da fasaha)
- David Jimkuta (Ci gaban jama'a)
- Ibrahim Lamido (Kiwon Lafia na Matakin Farko)
- Adaramodu Adeyemi (Wayar da kan Jama’a)
- Mustafa Saliu (Raya karkara)
Malaman musulunci sun bukaci Tinubu ya cire sunan El-Rufai cikin ministoci
A wani labarin kuma, mun ji cewa gamayyar kungiyar masu karatu da haddar Al-Qur'ani sun yi kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da kada ya rantsar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai a matsayin minista domin gaskiya, adalci, zaman lafiya da dorewar kasar.
Daraktan kula da harkokin ilimi a wata Gidauniya ta Sheikh Dahiru Bauchi wanda ya yi jawabi ga manema labarai a Bauchi a madadin malaman, Sheikh Sidi Aliyu Sise, ya bukaci Tinubu da ya yi taka-tsan-tsan sannan kada ya rantsar da azzaluman yan siyasa.
Asali: Legit.ng