Cire Tallafi: Gwamna Babagana Zulum Ya Raba Wa Magidanta 2,000 Buhunan Shinkafa a Maiduguri
- Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya yi rabon kayayyakin abinci a birnin Maiduguri
- Ya raba wa magidanta, mabuƙata kuma masu rauni buhuna 2,000 na shinkafa a matsayin tallafi
- Zulum ya ce an raba kayayyakin ne domin ragewa 'yan jihar raɗaɗin da suke ciki na cire tallafin man fetur da aka yi
Maiduguri, Borno - Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum, ya rabar da buhuna 2,000 na kayayyakin abinci ga al'ummar Mafoni da ke cikin birnin Maiduguri.
Mai taimakawa Gwamna Zulum kan harkokin yaɗa labarai Isa Gusau ne ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter.
Zulum ya raba kayayyakin domin ragewa mutane raɗaɗi
Gusau ya ce Zulum ya raba kayayyakin abincin ne a ƙoƙarinsa na ragewa mutane raɗaɗin da cire tallafin man fetur ya jefa su ciki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An gudanar da rabon kayayyakin ne a farfajiyar kwalejin karatun shari'a da na addinin Muslunci (MOGCOLIS) da ke birnin na Maiduguri.
Ya ce an bai wa kowane magidanci buhunan shinkafa biyu da kuma na wake guda ɗaya.
Zulum ya godewa Shugaba Tinubu da Kashim Shettima
Da yake jawabi ga mutanen da aka bai wa tallafin abincin, Zulum ya bayyana cewa kayayyakin da aka raba wani ɓangare ne na manyan motoci biyar na buhunan shinkafa 3,000 da Tinubu ya bai wa jihar ta Borno.
Gwamnan ya godewa Shugaba Tinubu da Kashim Shettima bisa namijin ƙoƙarin da suka yi na kawo wa jihar kayayyakin abinci don tallafawa jihar daga raɗaɗin cire tallafin man fetur.
Ya yi kira ga al'ummar jihar da su bai wa gwamnatinsa haɗin kai a yayin da yake ƙoƙarin ganin ya yi duk abinda ya kamata wajen rage musu raɗaɗin da suke ciki.
Da Dumi-Ɗumi: Maryam Shetty Ta Maida Martani Bayan Shugaba Tinubu Ya Maye Gurbinta a Jerin Ministoci
Tinubu ya yi bayani kan ainihin dalilin cire tallafin man fetur
Legit.ng a baya ta kawo rahoton da ke magana kan haƙiƙanin dalilin cire tallafin man fetur da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana.
Shugaban ya ce a aljihun wasu 'yan tsirarun mutane kuɗaɗen tallafin man da ake ba da wa yake zurarewa a duk sanda aka bayar da su.
Asali: Legit.ng