Jam'iyyar NNPP Ta Dakatar Da Sakatarenta Na Kasa Daga Mukaminsa
- Jam'iyya mai kayan marmari ta New Nigeria Peoples Party (NNPP) ta dakatar da sakatarenta na ƙasa daga kan muƙaminsa
- Shugabannin jam'iyyar na gunduma ta 5 a jihar Ogun su ne suka dakatar da Oladipupo Olayokun daga jam'iyyar kan wasu zarge-zarge da ake masa
- Shugabannin sun zargi Oladipupo da cin dunduniyar jam'iyyar tare da kitsa rikicin da ya addabi jam'iyyar a jihar Ogun
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Ogun - Jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ta dakatar da sakatarenta na ƙasa, Oladipupo Olayokun, bisa zargin cin dunduniyar jam'iyyar da sauran laifuka.
Olayokun, wanda yana daga cikin mambobin kwamitin gudanarwa na jam'iyyar (NWC), shugabannin jam'iyyar na gunduma ta 5 a ƙaramar hukumar Abeokuta ta Kudu a jihar Ogun ne suka dakatar da shi, cewar rahoton The Punch.
Dakatarwar da aka yi masa tana ƙunshe ne a cikin wata wasiƙa da aka aike masa a ranar 6 ga watan Agusta mai taken 'Takardar dakatarwa'.
Wasiƙar wacce take ƙunshe da laifukan da ake tuhumarsa da su, ta samu sa hannun shugabannin jam'iyyar 25 da mambobin jam'iyyar 25 na gundumar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
An tura wa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NNPP, Dr Rabiu Musa Kwankwaso da wanda ya kafa jam'iyyar Dr. Boniface Aniebonam kwafin takardar dakatar da Olayokun.
Laifukan da ake tuhumar Oladipupo da su
A cikin wasiƙar, an zargi Olayokun da cin dunduniyar jam'iyyar, sakaci kan muƙaminsa da ƙarfafa gwiwar kawo ruɗani a cikin jam'iyyar.
Jam'iyyar ta kuma zargi Olayakun da kitsa rikicin da yake faruwa na jam'iyyar a jihar Ogun, rahoton The Guardian ya tabbatar.
Wani ɓangare na wasiƙar na cewa:
"An dakatar da kai ne saboda nuna halin ko in kula kan harkokin jam'iyyar NNPP a matakin gunduma, inda ba ka taɓa halartar wani abu da ya danganci jam'iyya ba."
"Haka kuma ƙin zaɓar ɗan takarar shugaban ƙasa da na gwamna na jam'iyyar NNPP a zaɓen da ya gabata, rashin ladabi ne wanda dole a hukunta ka a kai."
Ganduje Ya Fadi Dalilin Rashin Ganin Kwankwaso Cikin Minitoci
A wani labarin kuma, shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya feɗe biri har wutsiya kan dalilin rashin ganin sunan Rabiu Musa Kwankwaso a cikin ministocin Tinubu.
Ganduje ya bayyana cewa dama azarɓaɓin tsohon gwamnan ne kawai ya sanya shi cewa zai samu muƙami a gwamnatin Tinubu.
Asali: Legit.ng