Ganduje Ya Yi Wa Kwankwaso Shagube Kan Batun Dawowarsa Jam'iyyar APC

Ganduje Ya Yi Wa Kwankwaso Shagube Kan Batun Dawowarsa Jam'iyyar APC

  • A wani yunƙurin ƙara fusata ƴan ɗariƙar Kwankwasiyya, Ganduje ya yi wa Rabiu Musa Ƙwankwaso ta yin dawowa jam'iyyar APC
  • Shugaban na jam'iyyar APC ta ƙasa ya bayyana cewa yanzu Kwankwaso yana da damar da zai iya dawowa jam'iyyar tun da shi ne kan madafun ikon ta
  • Ganduje ya kuma bayyana dalilin da ya sanya babu sunan Kwankwaso cikin ministocin Tinubu duk kuwa da kamun ƙafar da ya yi

Jihar Kano - Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa lokaci ya yi da yakamata Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya dawo jam'iyyar APC.

Kwankwaso ya fice daga jam'iyyar APC zuwa jam'iyyar Peoples democratic Party (PDP), kafin sake shillawa zuwa jam'iyyar New Nigerian People Party (NNPP), inda ya yi takarar shugaban ƙasa a babban zaɓen 2023.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Shugaban APC Na Jihar Arewa Ya Yi Murabus Awanni Bayan Nada Ganduje

Ganduje ya yi wa Kwankwaso shagube
Ganduje ya ce kofa a bude take idan Kwankwaso na son dawowa APC Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR
Asali: Facebook

Tsohon gwamnan na jihar Kano ya bayyana cewa yanzu da yake kan madafun ikon jam'iyyar APC, Kwankwaso zai iya tattaro kayansa ya dawo jam'iyyar, rahoton Daily Trust ya tabbatar.

Ganduje ya yi wa Kwankwaso shagube

Ganduje ya bayyana hakan ne dai yayin tattaunawa da wasu manema labarai a birnin Kano, ranar Asabar da daddare, cewar rahoton Eagle Online.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A kalamansa:

"Babu wanda zai ce Kwankwaso ba ɗan siyasa ba ne mai kyau, ko ba komai ya taɓa yin gwamnan Kano sau biyu, duk da dai ba a jere ba. Ya yi ministan tsaro duk da cewa bai san menene tsaro ba, sannan ya taɓa zama Sanata, duk da cewa bai taɓa cewa ko uffan ba a lokacin da ya kwashe a majalisa.
"Amma idan yana son dawowa APC, ƙofa a buɗe take musamman yanzu da wani wanda ga fito daga jiharsa shi ne shugaban jam'iyya, zai samu sauƙin yin kamun ƙafa."

Kara karanta wannan

Atiku Ya Yi Tsokaci Game Da Juyin Mulkin Nijar, Ya Fadi Matakan Da Ya Kamata ECOWAS Ta Ɗauka

Da aka tambayi Ganduje ko meyasa ba a ga sunan Kwankwaso ba a cikin jerin sunayen ministocin Shugaba Tinubu ba, sai ya kada baki ya ce dama tun farko a bakin Kwankwaso aka fara jin maganar naɗin ba daga wajen Tinubu ba.

Ganduje Ya Fadi Dalilin Cire Sunan Maryam Shetty

A wani labarin kuma, shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Gandije ya bayyana dalilin da ya sanya aka cire sunan Maryam Shetty, daga cikin ministocin Tinubu.

Ganduje ya bayyana cewa ƙorafin da aka yi ta yi a soshiyal midiya kan naɗin da aka yi mata, ya taka rawar gani wajen cire sunanta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng