Shin Da Gaske Sojoji Sun Kewaye Gidan Fashola Abuja? Hadimin Sanwo-Olu Ya Yi Martani
- Wani magoyin bayan dan takarar shugaban kasa, Peter Obi ya wallafa cewa sojoji sun kange gidan Babatunde Fashola a Abuja
- Jubri Gawat, mai ba wa gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu shawara kan yadda labarai ya musanta wannan zance
- Don tabbatar da haka, Gawat ya wallafa faifan bidiyo da ke nuna Fashola a wurin liyafa a Abuja da Sanata Gbenga Ashafa ya shirya
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT, Abuja - Akwai jita-jitar cewa sojoji sun kange mashigar gidan tsohon ministan Buhari, Babatunde Fashola da ke Abuja.
Wani magoyin bayan dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labour, Peter Obi, @BishopPOEvang shi ya wallafa haka a shafinsa na Twitter.
Ya ce sojoji sun kange mashigar gidan Babatunde Fashola yadda babu wanda zai iya shiga ko fita, Legit.ng ta tattaro.
Yadda sojoji suka kewaye gidan Fashola a Abuja
Ya ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Sojojin Najeriya sun kange mashigar gidan Babatunde Raji Fashola da ke Abuja.
"Baki da masu ziyara ba sa shiga ko fita daga gidan."
Hadimin Sanwo-Olu ya yi martani kan jita-jitar
A martanin shi, Jubril Gawat, babban mai ba wa gwamnan jihar Legas shawara a kan yada labarai ya karyata labarin da cewa:
"Mutumin da ya baje tare da holewa a liyafar Ashafa...wasa ku ke yi."
Wallafawar na fadin cewa Fashola ya halarci liyafar da tsohon majalisar Dattawa, Sanata Gbenga Ashafa ya shirya a ranar.
Gawat ya kara tabbatar da haka da faifan bidiyo inda Fashola ke taka rawa a liyafar.
Martanin jama'a kan jita-jitar:
balogin:
"Za su tashi ne kawai su shirya karya don masu goyon bayansu babu tunani su yi ta yadawa."
@belloadetunjii:
"Walahi wannan karairayi na 'Obidiot' ya yi yawa, matsananciyar damuwa ta koma wani abu daban."
@yomidada:
"Kar ku damu da su, suna shirya karya don a yi ta yadawa, abin dariya ne, na rasa meye su ke samu a kan haka."
Ya Na Daf Da Sauka, Fashola Ya Ce Sun Samar Wa Mutum 383,431 Aiki A Najeriya
A wani labarin, ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola da ke daf da sauka daga kujerar minista ya bayyana irin kokarin da su ka yi.
Ya ce gwamnatin Muhammadu Buhari ta yi abin da ba a taba yi ba a kasar wurin inganta rayuwar al'umma.
Ya ce gwamnatinsu ta samar wa mutane da dama hanyar da za su ci abinci a lokacin mulkinsu.
Asali: Legit.ng