Kano: Abubuwa 5 Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Maryam Shetty Da Tinubu Ya Sauya Sunanta
- Shugaba Bola Tinubu ya sauya sunan Maryam Shettima da Dakta Mariya Mahmoud a mukamin minista daga jihar Kano
- Tinubu ya zabi Shetty ne a ranar Laraba 2 ga watan Agusta kafin daga bisani ya sauya sunanta a yau Juma’a
- Shetty, bayan nada ta mukamin ministan, mutane sun yi ta cece-kuce a kai inda su ke ganin ba ta cancanta ba
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Kano – Kwanaki biyu bayan an saka sunan Dakta Maryam Shettima da aka fi sani da Shetty a jerin sunayen ministoci, Shugaba Tinubu ya sauya sunanta a yau Juma’a.
Tinubu ya sauya sunanta da Dakta Mariya Mahmoud wacce tsohuwar kwamishina ce a jihar Kano lokacin mulkin Abdullahi Umar Ganduje.
Punch ta tattaro cewa a ranar Alhamis 3 ga watan Agusta kafafen yada labarai sun dauki dumi inda wasu ke yabon nadin Shetty yayin da wasu kuma ke kushe Tinubu a kan nadin nata.
Jerin Ministoci: Dalilin Da Yasa Tinubu Ya Maye Gurbin Maryam Shetti Da Abokiyar Karatunta Mariya Mahmoud
Ga jerin abubuwa biyar da ya kamata ku sani game da Maryam Shettima Ibrahim:
1. Asalin sunanta shi ne Dakta Maryam Shettima Ibrahim wacce aka fi sani da Maryam Shetty.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
2. An haife ta a ranar 8 ga watan Afrilu na shekarar 1979. Yanzu haka ta na da shekaru 44 kenan a duniya, cewar BBC.
3. Shetty ta kasance ‘yar siyasa kuma mai rajin kare hakkin al’umma. Shetty ita ce shugabar kungiyar #WeBelieve wacce kungiya ce ta jam’iyyar APC.
4. Shetty ta kammala karatun jami’a a Bayero da ke Kano inda ta karanta harkar kula da kashi na dan Adam. Ta kuma yi digiri na biyu a sashen kula da kashi a jami’ar London ta Gabas.
5. A baya an taba zabanta inda wakilci Najeriya a babban taron Majalisar Dinkin Duniya (UN), Tori News ta tattaro.
Bidiyo: Yadda Maryam Shetty Ta Samu Labarin Cire Sunanta a Cikin Majalisa, Abinda Ta Yi Ya Ja Hankali
Tinubu Ya Janye Maryam Shetty, Ya Maye Ta Da Mariya Mahmud Daga Kano
A wani labarin, Shugaba Tinubu ya maye gurbin Maryam Shetty da Dakta Mariya Mahmoud a mukamin minista daga jihar Kano.
Tinubu ya sake mika jerin sunayen ministoci 19 a ranar Laraba 2 ga watan Agusta zuwa majalisar Dattawa.
A yau Juma'a 4 ga watan Agusta shugaban ya sauya sunan Shetty da ake ta cece-kuce a kanta.
Asali: Legit.ng