Ministoci: Yawan Mutanen Da Kowane Shugaban Najeriya Ya Nada Daga 1999 zuwa 2023
Shugaba Bola Tinubu ne shugaban Najeriya da ya fi kowane yawan ministoci tun farkon jamhuriya ta huɗu, wacce ta fara a 1999.
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Da farko dai shugaban ya aika da sunayen mutane 28 zuwa Majalisar Dattawan Najeriya a ranar Alhamis, 29 ga watan Yuli domin a tantancesu.
Ba a taɓa naɗa ministocin da suka kai yawan na Tinubu ba
Sai dai daga bisani kuma, Tinubu ya sake aikawa da kashi na biyu na mutanen da yake so ya bai wa muƙaman ministoci su 19, zuwa zauren majalisar a ranar Laraba, 2 ga watan Agusta.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Godswill Akpabio ne ya karanto sunayen mutanen 19 da Tinubu ya turo majalisar, wanda idan aka haɗa da na baya, sun tashi 47 kenan gaba ɗaya.
Jiga-Jigan APC 2 Kuma Makusantan Tinubu Sun Yi Magana Bayan Rashin Ganin Sunayensu a Jerin Ministoci
A wani rahoto na The Cable, an yi ittifaƙin cewa, ba a taɓa yin ministoci 47 ba a tarihin dimokuraɗiyyar Najeriya ba sai a wannan lokaci da Shugaba Tinubu ke shirin yi.
An nemi a rage yawan kuɗaɗen da ake kashewa wajen gudanar da gwamnati
'Yan Najeriya da dama sun yi kira da a rage yawan kuɗaɗen da ake kashewa wajen gudanar da harkokin gwamnatin ƙasar.
Wani mai sharhi kan al'amuran jama'a Okanlawon Gaffar a zantawarsa da Legit.ng, ya yi kira ga gwamnati da ta rage yawan kuɗaɗen gudanarwa, ta hanyar rage albashi da ma yawan ma'aikata.
Ya ce yanayin yadda ake tafiyar da ƙasar, ya nuna cewa da gumin talakawa ne ta dogara domin amfanin wasu 'yan tsirarun mutane.
Adadin ministocin da shugabannin Najeriya suka naɗa tun 1999
Ga takaitaccen bayani kan adadin ministocin da kowane shugaban ƙasa tun daga 1999 zuwa yau, ya naɗa a lokacin wa'adinsa.
Shugabannin kasa | Adadin ministocinsu |
Shugaba Bola Ahmed Tinubu | Ministoci 47 |
Tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari (2019) | Ministoci 42 |
Tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari (2015) | Ministoci 36 |
Tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan (2011) | Ministoci 33 |
Tsohon shugaban ƙasa Umar Musa Yar'adua (2007) | Ministoci 39 |
Tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo (2003) | Ministoci 40 |
Tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo (1999) | Ministoci 27 |
Jerin jihohin da Tinubu ya ba ministoci biyu ko fiye da haka
Legit.ng a baya ta yi rahoto kan wasu jihohi da Shugaba Tinubu ya gwangwaje da kujerun ministoci guda biyu ko fiye da haka.
Wasu na ganin bayar da muƙamin minista fiye da guda ɗaya da shugaban ya yi a wasu jihohin ba zai rasa nasaba da irin gudummawar da suka ba shi lokacin zaɓe ba.
Asali: Legit.ng