Jam'iyyar APC Ta Zabi Ganduje A Matsayin Shugabanta Na Kasa
- Jam'iyyar APC mai mulki ta zabi tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje a matsayin shugabanta na kasa
- An tabbatar da nadin Ganduje ne yayin babban taron kwamitin masu ruwa da tsaki na jam'iyyar a Abuja
- Har ila yau, an nada Ajibola Basiru a matsayin sakataren jam'iyyar na kasa da zai maye gurbin Iyiola Omisore
FCT, Abuja - Jam'iyyar APC mai mulki ta zabi tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje a matsayin shugaban jam'iyyar na kasa.
Jam'iyyar ta tabbatar da zaben Ganduje ne a yau Alhamis 3 ga watan Agusta yayin taron masu ruwa da tsaki a Abuja.
Har ila yau, jam'iyyar ta zabi Ajibola Basiru a matsayin sakataren jam'iyyar na kasa, gidan talabijin na Channels ta tattaro.
An zabi Ganduje da Basiru a matsayin shugaba da kuma sakataren APC
An zabi Ganduje da Basiru ne yayin ganawar kwamitin karo na 12 a dakin taro na Transcorp Hilton da ke Abuja, cewar The Guardian.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Shugaban kasa, Bola Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima da sauran jiga-jigan jam'iyyar APC sun samu halartar ganawar.
Wadanda ba su samu halartar taron ba akwai tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari da tsohon mataimakinsa, Yemi Osinbajo.
Har ila yau, tsohon shugaban jam'iyyar APC na farko, Bisi Akande shi ma bai samu halartar ganawar ba, Vanguard ta tattaro.
Tinubu ya shawarci masu mulki su cika alkawuran da su ka dauka
Yayin da ya ke jawabi, Tinubu ya ce jam'iyyar APC yanzu ta yi nasara saura kuma ta cika dukkan alkawuran da ta dauka wa al'ummar kasar.
A watan Yuli ne dai shugaban jam'iyyar, Sanata Abdullahi Adamu da sakataren jam'iyyar, Iyiola Omisore su ka yi murabus daga mukaminsu.
An yi ta rade-radin cewa murabus din Sanata Adamu bai rasa nasaba da irin taron dangi da 'yan bangaren Shugaba Tinubu su ka yi masa.
Shugaban APC Ya Hakura Da Rikon Jam’iyya, Ya Sauka Daga Mukaminsa
A wani labarin, ana ta yada jita-jita cewa shugaban jam'iyyar APC, Sanata Abdullahi Adamu ya sauka daga mukaminsa.
Rahotanni sun tabbatar cewa an jiyo daga majiya mai karfi na cewa Sanatan ya ajiye mukaminsa saboda wasu dalilai.
Asali: Legit.ng