Bayani Kan Ministocin Da Tinubu Ya Bada Sunayensu Da Shiyyoyin Da Suka Fito
- Jerin sunayen mutanen da Tinubu ya fitar na baya-bayan nan ya gwada cewa Tinubu na mayar da alkhairi ga wanda ya hidimta ma sa
- Za a iya tabbatar da hakan idan aka yi la'akari da yadda Tinubu ya yi rabon mukamansa a bangarori daban-daban na kasar nan
- Shiyyar Arewa maso Yamma, wacce ta fi kowace bai wa Tinubu kuri'u, ita ce ta fi kowace shiyya samun yawan ministoci
FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Tinubu ya mika sunayen rukuni na biyu na ministocinsa ga Majalisar Dattawa domin tantancewa da tabbatarwa.
A kashi na biyu na jerin sunayen ministoci, Shugaba Tinubu ya gabatar da sunayen mutane 19, wanda yanzu yawansu gaba daya ya kai 47.
Mutanen da jerin sunayen ministocin na Tinubu ya kunsa
Jerin sunayen da aka fitar ya kunshi tsofaffin gwamnoni, masana, ‘yan majalisu da wasu fitattun ‘yan siyasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai kuma bincike ya nuna cewa shugaban kasar ya nada ministoci daga wasu shiyyoyin bisa la’akari da yawan kuri’un da suka ba shi.
A zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu, yankin Arewa maso Yamma ya bai wa jam’iyyar APC da dan takararta, Bola Tinubu kuri’u mafi yawa, wanda hakan ya ba shi nasarar lashe zabe.
Wani bincike na jaridar The Cable, ya nuna cewa Shugaba Tinubu ya samu kashi 30% na kuri’unsa ne daga yankin Arewa maso Yamma, yayin da yankin Kudu maso Gabas ya bashi mafi karancin kuri’u.
Tinubu ya sakawa wadanda suka hidimta ma sa da mukaman ministoci
Da yake tsokaci kan jerin sunayen, MS Ingawa, wani mai sharhi kan al'amuran jama'a, ya ce an san Bola Ahmed Tinubu da iya gano hazikan mutane da kuma sakawa wadanda suka hidimta ma sa.
Ga bayanin yadda kowane yanki ya zabi shugaba Tinubu a zaben 2023 da ya gabata, da kuma adadin ministocin da suka samu.
Shiyya | Yawan kuri'u | Kaso cikin 100 | Ministoci |
Arewa maso Yamma | 2,652,235 | 30% | 10 |
Kudu maso Yamma | 2,542,979 | 25.9% | 9 |
Arewa ta Tsakiya | 1,760.993 | 20% | 8 |
Arewa maso Gabas | 933,176 | 13.5% | 8 |
Kudu maso Kudu | 799,957 | 9.1% | 7 |
Kudu maso Gabas | 127,605 | 1.5% | 5 |
Jihohin da Shugaba Tinubu ya bai wa ministoci guda 2
Legit.ng a baya ta kawo rahoto kan sunayen mutanen da Shugaba Bola Tinubu ya zabo a matsayin wadanda zai bai wa ministoci.
Akalla ko wace jiha daga cikin jihohi 36 ciki har da FCT da muke da su, ta samu mutum daya da za a nada a matsayin minista. Sai dai akwai jihohin da suka yi sa'ar samun mutane biyu cikin wadanda za a bai wa mukamin ministoci.
Asali: Legit.ng