Shugaba Bola Tinubu Da Shugabannin APC Sun Shiga Taron NEC
- Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya jagoranci taron majalisar zartaswa ta ƙasa (NEC) ta jam'iyyar All Progressives Congress (APC)
- Taron na majalisar zartaswar na zuwa ne a daidai lokacin da jam'iyyar take fama da rikicin shugabanci bayan murabus ɗin Sanata Abdullahi Adamu
- A wajen taron na NEC, wasu majiyoyi sun bayyana cewa za a zaɓi tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje a matsayin shugaban jam'iyyar
FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da jiga-jigan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) sun shiga taron majalisar zartaswa (NEC) karo na 12 na jam'iyyar.
Zuwan shugaban ƙasa Bola Tinubu da misalin ƙarfe 12:30 na rana, ya sanya aka fara gudanar da taron wanda yake gudana a ɗaƙin taro na otel ɗin Transcorp Hilton, a birnin tarayya Abuja, rahoton The Nation ya tabbatar.
Mambobin majalisar zartaswar sun fara isa ɗaƙin taron tun misalin ƙarfe 9:30 na safe, inda muƙaddashin shugaban jam'iyyar Sanata Abba Kyari da sauran mambobin kwamitin gudanarwa na ƙasa (NEC) na jam'iyyar ke wurin domin tarbar mahalarta taron.
Abubuwan da taron zai yi duba a kansu
Taron dai zai yi duba ne kan muhimman batutuwa guda biyar domin amincewa da su.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Batutuwan sun haɗa da naɗa masu binciken kuɗi daga waje, cike gurabun muƙaman dake da giɓi, naɗa shugaban jam'iyya da naɗa sakataren jam'iyya na ƙasa da sauran batutuwa.
Majiyoyi a wajen taron sun nuna cewa akwai yiwuwar za a zaɓi tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, a matsayin muƙaddashin shugaban jam'iyyar na ƙasa, cewar rahoton Daily Trust.
Idan ba a manta ba dai shugaban jam'iyyar da sakataren jam'iyyar na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu da Iyiola Omisore, sun yi murabus daga kan muƙamansu.
Ƙasa da sati ɗaya bayan murabus ɗin su, mataimakin shugaban jam'iyyar na ƙasa (yankin Arewa maso Yamma), Salihu Mohammed Lukman, ya sauka daga kan muƙaminsa.
Osinbajo Bai Halarci Taron NEC Ba
A wani labarin kuma, tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo bai samu halartar taron NEC na APC ba.
Osinbajo ya bayyana cewa ba zai samu halartar taron ba ne saboda yana ƙasar waje domin gudanar da wasu aikace-aikace.
Asali: Legit.ng