Maryam Shetty: Nadin Jikar Sarkin Kano a Cikin Ministoci Ya Jawowa Tinubu Surutu
- Dr. Maryam Shettima ce ta samu daya a cikin guraben Ministocin da ake sa ran a nada daga Kano
- Matashiyar ‘Yar siyasar ta fito ne daga gidan sarauta, ta na cikin ‘yan matan da APC ta ke ji da su
- Hakan bai sa mutane sun yabawa Bola Tinubu, Kanawa da-dama sun soki zabin shugaban kasar
Kano - Maryam Shettima ta na cikin jerin Ministocin da Mai girma Bola Ahmed Tinubu yake so ya nada a gwamnatinsa, za ta wakilci jihar Kano.
Legit.ng Hausa ta lura zabin Dr. Maryam Shettima (Shetty) ya jawo surutu daga mutane a lokacin da matasa da mata ke kukan ba a damawa da su.
Tsohuwar ma’aikaciyar asibitin ta na cikin mata da matasan da ake ji da su sosai a jam’iyyar APC.
Wacece Maryam Shetty?
Politics Digest ta kawo rahoto cewa Maryam Shetty ta na sha’awar siyasa da taimakawa al’umma, mace ce mai rajin ba matasa mukamai.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Bayan kasancewarta cikin kwamitin yakin neman zaben BolaTinubu/Kashim Shettima, ‘yar siyasar ta tallata tikitin Gawuna/Garo a jihar Kano.
Kafin yanzu, Shetty ta kasance cikin magoya bayan tsohon shugaba Muhammadu Buhari, su ne silar kafa kungiyar nan ‘We Believe’ da ta kare shi.
Jikar Sarkin Kano Ado Bayero
Rahoton ya ce wanda ake so ta zama Ministar jika a ce a gidan Sarki Marigayi Ado Bayero. Dr. Maryam Shetty ‘ya ce ga Sarakunan Kano da Bichi.
‘Yar siyasar ta karanci ilmin gashin kashi da tausa a jami’ar Bayero da ke Kano, sannan tayi digirgir daga jami’ar East London da ke Stratford.
A birtaniya, ta kware ne a bangaren kula da masu wasanni. Hakan ya jawo tayi aiki a kasar waje bayan ta barasibitin kashi da ke Dala a jihar Kano.
Ministar goben ta na cikin likitocin gasar Olympics da aka yi a Landan, ta duba manyan 'yan wasan Duniya irinsu Usain Bolt a wancan lokaci.
Shetty ta samu shiga, an jefar da jiga-jigai
A lokacin da ake tunanin za a ga sunayen mutanen Abdullahi Umar Ganduje da Rabiu Musa Kwankwaso, sai aka ga Shetty da Abdullahi T. Gwarzo.
A yayin da na-kusa da ita da sauran wadanda su ka san labarin gwagwarmayar ta su ke yabawa Bola Tinubu, akwai masu yin martani akasin hakan.
Alakar NNPP da APC ta wargaje?
A baya rahotonmu ya nuna kofa a bude ta ke ga Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ko kuwa wani daga cikin ‘ya ‘yan NNPP su samu kujera a majalisar FEC.
An sa ran Shugaban kasa zai aikawa Majalisar dattawa wani daga cikin mutanen tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje karin sunayen da za a tantance.
Asali: Legit.ng