Labari Da Dumi-Dumi: Tinubu Ya Nada Atiku, Lalong, Matawalle a Karin Ministoci 19
- ‘Yan Majalisar Dattawa za su cigaba da tantance ragowar wanda ake so su zama Ministoci a kasar nan
- Bola Tinubu ya aiko sunayen wadanda ya zaba, a ciki akwai wasu tsofaffin Gwamnonin jihohi biyar
- A cikin wadanda aka zaba akwai Farfesa ahir Mamman OON, SAN da Sanata Aliyu Sabi Abdullahi
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abuja - Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya karanto karin Ministocin da ake sa ran za a nada bayan an tantance su.
Channels TV ta kawo rahoto cewa akwai tsofaffin Gwamnonin jihohin APC a cikin jerin.
Daga ciki akwai Gboyega Oyetola (Osun), Simon Lalong (Filato), Bello Matawalle (Zamfara) da Atiku Abubakar Bagudu (Kebbi).
Har ila yau akwai Ibrahim Geidam wanda ya yi Gwamnan Yobe daga shekarar 2010 bayan rasuwar Mamman Ali har zuwa 2019.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Kamar yadda Daily Trust ta ce, akwai mutane 19 a cikin sahu na biyu na ragowar zababbun mutanen da za a tantance a majalisa.
A jerin akwai Ahmed Tijani, Dr Isiaka Salako, Dr Tunji Alausa da Tanko Sunisi da kuma jagorar mata a APC, Dr. Maryam Shetti.
Har ila yau, za a tantance Lola Ade John, Abubbakar Audu, Sabi Abdullahi, Alkali Samani a cikin wadanda za su rike mukaman.
A sunayen da aka gabatar a yauakwai matashin ‘dan kasuwan nan, Olatunbosun Tijani da tsohon ‘dan majalisa, Tanko Sununu.
Akwai fitaccen likitan koda, Dr. Tunji Alausa a jerin sababbin Ministocin da za su shiga ofis idan sun samu tantacewar majalisa.
Sanata Saidu Alkali Ahmed da Sanata Aliyu Sabi su na cikin wadanda za a tantance,
Cikakken jerin Ministocin
Wani daga cikin magoya bayan jam'iyyar APC mai-mulki, Malam Imran Muhammad ya tattaro sunayen a shafinsa na Twitter dazu.
- AHMED TIJJANI
- BOSUN TIJJANI
- DR MARYAM SHETTI
- ISHAK SALAKO
- TUNJI ALAUSA
- TANKO SUNUNU
- ADEGBOYEGA OYETOLA
- ATIKU BAGUDU
- BELLO MATAWALLE
- IBRAHIM GEIDAM
- SIMON BAKO LALONG
- LOLA ADEJO
- SHUAIBU ABUBAKAR
- TAHIR MAMMAN
- ALIYU SABI
- ALKALI AHMED
- HEINEKEN LOKPOBIRI
- UBA MAIGARI
- ZEPHANIAH JISSALO
Asali: Legit.ng