A Karshe, Shugaban Majalisa Ya Karanto Sunayen Ragowar Ministocin da Za a Nada
- A yau mutanen Najeriya za su san su wanene sauran wadanda za su shiga jerin ragowar Ministocin kasa
- Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila ya gabatar da sahun karshe na Ministocin
- Ana tunanin yau ya dace a gama tantance sahun farko na mutanen da Bola Tinubu ya fara aiko sunayen su
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abuja - Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila ya aikowa majalisar dattawa sunayen ragowar Ministoci.
Rahoton da mu ka samu daga tashar Channels TV ta ce Rt. Femi Gbajabiamila ya iso majalisar tarayyar da jerin sunayen ne yanzu nan.
Da kimanin karfe 3:19 aka ga tsohon shugaban majalisar wakilan tarayyan ya shigo zauren majalisa dauke da wasikar shugaban kasa.
Femi Gbajabiamila ya hadu da Godswill Akpabio
A yayin da Gbajabiamila ya mikawa Godswill Akpabio sunayen, ana tsakiyar tantance Lateef Fagbemi SAN wanda yake sahun farko.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Daily Trust ta ce zuwa yanzu ba a san adadi ko karin bayani game da wadanda aka zaba ba.
Rahoton ya ce Mai shugaban kasa shawara a kan harkokin majalisa, Sanata Ibrahim Hassan Hadejiya ya rako Gbajabiamila zuwa majalisar.
Jihohi 11 ba su da Ministoci tukuna
Abin da ake za rai shi ne za a ji sunayen Ministocin da aka zabo daga Adamawa, Bayelsa, Gombe, Kano, Kebbi, Kogi, Legas da kuma Osun.
Ragowar jihohin da ba su da Ministoci su ne Yobe, Filato, Zamfara sai watakila birnin tarayya Abuja da mutanenta su ke rokon ba su kujera.
An kusa gama tantance 'yan sahun farko
Zuwa yanzu ana da labari an tantance mutane 25, ragowar mutum uku kadai su ka ragewa majalisar dattawan ta tantance a jerin farko.
Da Dumi-Dumi: FG Da NLC Sun Fara Tattaunawa Kan Shirin Rage Radadi Na Tinubu Bayan Cire Tallafin Man Fetur, Bayanai Sun Fito
Da ya je gaban majalisa a yau, an ji Mista Dele Alake ya yi bayanin gwagwarmayar da ya yi bayan zaben Marigayi MKO Abiola a Yunin 1993.
Karin Ministoci 19
Rahoto ya zo cewa karin sunayen Ministocin ya kunshi Simon Lalong, Gboyega Oyetola, Atiku Bagudu, Ibrahim Geidam da Bello Matawalle.
Ministocin za su wakilci jihohin Filato, Osun, Kebbi, Yobe da Zamfara a majalisar FEC.
- AHMED TIJJANI
- BOSUN TIJJANI
- DR MARYAM SHETTI
- ISHAK SALAKO
- TUNJI ALAUSA
- TANKO SUNUNU
- ADEGBOYEGA OYETOLA
- ATIKU BAGUDU
- BELLO MATAWALLE
- IBRAHIM GEIDAM
- SIMON BAKO LALONG
- LOLA ADEJO
- SHUAIBU ABUBAKAR
- TAHIR MAMMAN
- ALIYU SABI
- ALKALI AHMED
- HEINEKEN LOKPOBIRI
- UBA MAIGARI
- ZEPHANIAH JISSALO
Asali: Legit.ng