NLC Ta Bukaci N200k Matsayin Mafi Karancin Albashi Da Wasu Sharuda Domin Dakatar Da Zanga-Zanga

NLC Ta Bukaci N200k Matsayin Mafi Karancin Albashi Da Wasu Sharuda Domin Dakatar Da Zanga-Zanga

  • Kungiyar NLC ta bukaci a kara mafi karancin albashi zuwa N200,000 daga cikin sharuddan da suka gindaya na kawo karshen zanga-zangar da ke gudana
  • Ayuba Suleiman, shugaban kungiyar NLC a jihar Kaduna, ya ce sauran bukatun sun hada da gwamnati ta tabbatar da cewa ta gyara matatun man fetur da ake da su
  • Kungiyar ta kuma bukaci a mayar da farashin man fetur zuwa N185, wanda hakan ke nuna cewa gwamnati ta ci gaba da biyan kudaden tallafin man fetur kenan

Kaduna - Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC), reshen jihar Kaduna, ta bukaci a biya mafi karancin albashi na N200,000 tare da gyara matatun mai guda hudu.

Kungiyar ta kuma bukaci a dawo da farashin litar man fetur zuwa N185 muddun ana so ta kawo karshen zanga-zangar da ake ci gaba da yi ta nuna adawa da cire tallafin man fetur da Shugaba Bola Tinubu ya yi.

Kara karanta wannan

Cire Tallafi: "Ko Kobo Ba'a Ceto Ba" NLC Ta Maida Martani Mai Zafi Kan Kalaman Shugaba Tinubu

Shugaban NLC na jihar Kaduna, Ayuba Suleiman ne ya bayyana hakan kamar yadda Channels TV ta wallafa.

NLC ta fadi sharuɗan da take so a cika ma ta
NLC ta nemi a ƙara mafi ƙarancin albashi zuwa naira 200,000. Hoto: @NLCHeadquarters
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NLC ta shawarci gwamnati ta ci gaba da biyan kudin tallafin man fetur

Ayuba Suleiman, shugaban NLC na Jihar Kaduna, ya ce kungiyar na son a kara mafi karancin albashin ma'aikata zuwa N200,000 sabanin N30,000 da ake biya a baya.

Ayuba ya kuma yi kira ga gwamnati da ta yi kokarin sauke farashin man fetur zuwa naira 185 a duk lita da ake sayar da shi a baya.

Haka nan kuma ya shawarci gwamnati da ta ci gaba da biyan tallafin man fetur, sannan kuma ta tabbatar da ta kara mafi karancin albashin zuwa abinda aka bukata.

Me ye ya sa dole a cire tallafin man fetur?

A ranar 29 ga watan Mayu ne shugaba Bola Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur, inda nan take ‘yan kasuwa suka kara farashin man.

Kara karanta wannan

Bayan Taro a Aso Villa, NLC Ta Yi Magana Kan Janye Zanga-Zanga da Shiga Yajin Aikin da Ta Shirya a Najeriya

Gwamnati da wasu masu ruwa da tsaki sun sha cewa, Najeriya ba za ta iya ci gaba da ranto kudade ta na biyan tallafin ba.

Sai dai kungiyar kwadago bayan ganawa da gwamnati, ta ce matakin da Shugaba Tinubu ya dauka na dakile wahalhalun da cire tallafin ya jefa mutane ciki bai wadatar ba, inda ta nemi a kara mafi karancin albashi.

Ko ƙwandala ba a tara ba, NLC ta ƙalubalanci iƙirarin Shugaba Tinubu

Legit.ng a baya ta kawo muku rahoto kan iƙirarin Shugaba Tinubu, na cewa sun tara sama da tiriliyan ɗaya bayan cire tallafi, wanda NLC ta ce ba gaskiya ba ne.

Da yake jawabi yayin zanga-zangar da ƙungiyar ta NLC ke gudanarwa, shugaban ƙungiyar Joe Ajaero, ya ce kwamitin da gwamnatin ta kafa na sulhu tsakaninsu ya shaida musu cewa ba a tara komai ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng