"Idan Kana Sauraron Jawabin Tinubu, Za Ka Bukaci Fanka," Shehu Sani Ya Magantu Kan Jawabin Shugaban Kasa

"Idan Kana Sauraron Jawabin Tinubu, Za Ka Bukaci Fanka," Shehu Sani Ya Magantu Kan Jawabin Shugaban Kasa

  • Tsohon Sanata, Shehu Sani ya yi kakkausar suka kan jawabin da Shugaba Tinubu ya yi a jiya Litinin
  • Shehu Sani ya kwatanta jawabin da cewa ba shi da maraba da na tsohon shugaban kasa, Buhari
  • Tinubu ya yi jawabi a jiya ga 'yan kasa inda ya bayyana matakan da ya dauka akan tattalin arziki

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kaduna - Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani ya fadi abin da 'yan Najeriya su ke bukata yayin sauraron jawabin Shugaba Tinubu.

Tinubu ya yi jawabi ga 'yan kasa a jiya Litinin 31 ga watan Yuli yayin da mutane ke fama tsadar kayayyaki tun bayan cire tallafin mai.

Shehu Sani ya magantu kan jawabin Tinubu, ya ce mutum na bukatar fanka idan ya na sauraron jawabin
Shehu Sani Ya Magantu Kan Jawabin Shugaban Kasa, Ya Ce Mutum Na Bukatar Fanka Kafin Sauraran Jawabin. Hoto: Muhammad Buhari/Shehu Sani.
Asali: Facebook

Sani ya kwatanta jawabin Tinubu da cewa babu maraba da na Buhari

Sani ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter inda ya kwatanta jawabin da cewa ba shi da maraba da na tsohon shugaban kasa, Buhari.

Kara karanta wannan

Shugaba Bola Tinubu Ya Bayyana Babban Abin Da Ke Hana Shi Bacci Dare Da Rana

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce duk lokacin da 'yan Najeriya ke sauraron jawabin shugabanninsu, suna bukatar shayi mai zafi da fanka a gefensu.

Sani ya wallafa hakan a yau Talata 1 ga watan Yuli kamar haka:

"Lokacin da ka ke sauraron jawabin Buhari, ka na bukatar shayi mai zafi don kara maka kuzari, idan kuma na Tinubu ne fanka ka ke bukata."

Mutane sun yi martani akan kushe jawabin Tinubu da Shehu Sani ya yi:

Legit.ng ta tattaro muku martanin 'yan Najeriya a kan rubutun Shehu Sani.

@Boma_Wills:

"Dukkan su sun bambanta amma suna da alaka ta bangare daya. Babu komai a ciki sai zargi."

@OwoBalo:

"Rayuwa ba seti, damuwa ba ta karewa."

@mrlurvy:

"Amma idan ka saurari jawabin Shehu Sani ba ka bukatar gwajin jini."

@ayinlade3:

"Ta tabbata ka na sauraro da ido ne ba ta.."

Kara karanta wannan

Shehu Sani Ya Fadi Manyan Dalilai 13 Da Bai Kamata ‘Yan Najeriya Su Goyi Bayan Mamayar Jamhuriyar Nijar Ba

@laraGold143:

"Fankar ta zama dole don kawar da iskar shirme."

@xeenax08:

"Ya yi kyau Oga, ka fahimci dukkansu, amma jawabin wannan ya fi na baya, ko yadda ake maganar ta bambanta."

@DeliciousBea1:

"Zafi da kansa."

"8k Almajirantar Da Kasar Za Ta Yi”: Shehu Sani Ya Fadi Abin Da Mutane Za Su Yi Kan Tallafin Tinubu

A wani labarin, Sanata Shehu Sani ya soki shirin ba da tallafi da Shugaba Tinubu ke son bayarwa a Najeriya.

Sani ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter inda ya ce babu abinda kudin za su yi wa mutane.

Ya ce kudaden kara talauci kawai za su yi wa 'yan kasa, ya kwatanta kudaden da Buhari ya bayar a lokacinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.