Sanata Abbo Ya Bayyana Yadda Ya Kammala Firamare A Aji 3 Saboda Basirar Da Yake Da Shi
- Sanata mai wakiltar Adamawa ta Arewa, Ishaku Abbo ya bayyana yadda ya kammala firamare a aji uku
- Abbo ya bayyana haka a yau Litinin 31 ga watan Yuli yayin tantance ministoci a majalisar Dattawa a Abuja
- Ya ce ya rubuta jarrabawar kammala firamare a aji uku kuma ya yi nasara saboda iliminsa
FCT, Abuja - Sanatan Adamawa ta Arewa, Ishaku Abbo ya bayyana yadda ya rubuta jarrabawar kammala firamare a aji uku tare da yin nasara.
Abbo ya bayyana haka ne yayin tantance ministoci a majalisar Dattawa a yau Litinin 31 ga watan Yuli a Abuja, Legit.ng ta tattaro.
Yayin tantance minista daga jihar Benue Farfesa Joseph Utsev an samu hatsaniya kan shekarunsa da kuma lokacin da ya kammala firamare, cewar Punch.
Abin da jawo takaddamar da Sanatan ya fadi bayanin rayuwar karatunsa
A takardunsa, ya ce an haife shi a 1980 kuma ya kammala sakandare a 1989, inda Sanata Tokunbo Abiru daga jihar Lagos ya kalubalance shi, cewar gidan talabijin na Channels.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yayin da Sanata Abbo ya tashi don yiwa Farfesan tambaya, ya bayyana cewa shi ma ya na da irin wannan matsala irin ta Utsev.
Abbo ya ce ya rubuta jarrabawar kammala firamare kuma ya yi nasara a aji uku a firamare, inda ya ce ya kasance na daban a ajinsu, cewar Vanguard.
Ya fadi yadda ya samu nasara a jarrabawar firamare a aji uku
Ya ce:
"Da alamu wasu ba su fahimci abin ba, bari na fayyace muku wani abu da ya faru da ni akan irin haka.
"Na rubuta jarrabawar kammala firamare a aji uku kuma na yi nasara saboda ni na daban ne.
"Don haka maganan yaushe ka shiga makaranta ko kuma yaushe ka gama ko yaushe ka rubuta jarrabawar duk ba ta taso ba."
Sanata Abbo Ya Yi Martani Ga Hukuncin Kotu Da Ta Hana Shi Neman Takara A APC
A wani labarin, Sanata mai wakiltar Adamawa ta Arewa, Ishaku Abbo ya ce zai daukaka kara kan jam'iyyar APC da ta hana shi takara.
Abbo ya bayyana haka ne yayin martani bayan babbar kotun ta haramta masa tsayawa takara a jam'iyyar.
Yayin yanke hukuncin, Alkalin kotun, Mohammed Danladi ya bayyana cewa karamar hukumar Mubi ta Arewa ta kori Sanatan a ranar 7 ga watan Octoban 2022.
Asali: Legit.ng