Sunayen Ministocin Tinubu: Ainihin Dalilin Da Yasa Aka Zabi Wike Ya Fito Fili
- Tsohon ministan ayyuka, Sanata Adeseye Ogunlewe ya fadi dalilin ba wa Wike mukamin minista
- Ogunlewe ya bayyana haka ne a ranar Lahadi 30 ga watan Yuli yayin hira da gidan talabijin na Channels
- Ya ce kowa yasan irin sadaukarwa da Wike ya yi lokacin zabe don tabbatar da cewa APC ta yi nasara
FCT, Abuja - Tsohon ministan ayyuka Sanata Adeseye Ogunlewe ya fadi dalilin da yasa aka nada Nyesom Wike a matsayin minista.
Adeseye ya rike ministan ayyuka ne a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, Legit.ng ta tattaro.
Sanatan ya bayyana dalilin nada Wike minista da Tinubu ya yi
Sanata Ogunlewe ya bayyana haka ne a jiya Lahadi 30 ga watan Yuli yayin hira da gidan talabijin na Channels.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya ce dalilin ba wa tsohon gwamnan jihar Rivers mukamin minista shi ne don a saka masa da kokarin da ya yi wa APC lokacin zabe.
Wike wanda ya kasance dan jam'iyyar PDP ne ya marawa dan takarar jam'iyyar APC, Bola Tinubu saboda matsalar sa da shugabannin PDP.
Ya ce kowa yasan irin sadaukarwa da Wike ya yi a zaben da ya gabata
Ya ce:
"Wannan abu ne mai sauki da kowa zai fahimta, idan ka bibiyi abin da ya faru a zaɓen da ya gabata kasan ya kamata a sakawa Wike da irin gudummawar da ya bayar."
Ya ce Wike ba shi kadai ba ne ya yi wa APC aiki a zaben da ya gabata, BusinessDay ta tattaro.
Ya bayyana tsohon gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi da na Kaduna, Nasiru El-rufai da cewa an ba su mukamin ne saboda irin gwagwarmayar da suka yi wa APC.
"Shugaba Tinubu Ba Zai Yi Dana Sanin Nada Ni Minista Ba", Jawabin Wike Yayin Tantance Shi a Majalisa
Sanatan ya ce ya yi imani Umahi na bukatar wannan mukami ganin irin yadda ya samar da abubuwan ci gaban kasa jiharsa.
Tsohon Bidiyon Wike Yana Cewa Ba Zai Yi Minista Ba Ya Tada Kura A Intanet
A wani labarin, tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike ya bayyana cewa ba ya bukatar zama minista.
Wike ya bayyana haka ne a wani tsohon bidiyo da ya karade kafafen sadarwa a lokacin zabe.
Wannan na zuwa ne bayan Shugaba Bola Tinubu ya nada shi mukamin minista da za a fara tantacewa a ranar Litinin 31 ga watan Yuli.
Asali: Legit.ng