Ganduje Ya Kara Samun Gagarumin Goyon Baya Na Zama Shugaban APC Ta Kasa
- Tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje na ci gaba da samun karɓuwa a matsayin wanda zai gaji shugaban APC
- Dattawan APC na Arewa ta Tsakiya sun ayyana goyon bayansu ga Ganduje ya zama muƙaddashin shugaban APC
- A cewarsu, sun amince tsohon gwamnan ya maye gurbin Adamu amma bisa sharaɗin na riƙon kwarya ƙafin babban taro
Janar Lawrence Onoja, taohon hadimin tsohon shugaban ƙasa a mulkin soja, Marigayi Sani Abacha da wasu dattawan APC a Arewa ta Tsakiya, sun bayyana wanda suke bayan ya zama shugaban APC.
Jaridar Punch ta rahoto cewa jiga-jigan sun goyi bayan tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya maye gurbin tsohon shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Adamu.
Sai dai dattawan APC na shiyyar sun kafa sharaɗin cewa sun aminta Ganduje ya maye gurbin Adamu amma a matsayin mukaddashi shugaban jam'iyya har sai an gudanar da babban taron kasa, Vanguard ta rahoto.
Yadda Ganduje ya samu karbuwa a shiyyoyin arewa
Wannan na zuwa ne kwana uku kacal bayan shugabannin APC na jihohi 7 a shiyyar Arewa maso Yamma, sun ayyana goyon bayansu ga Ganduje a wani taro da suka gudanar a Kaduna.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Haka zalika gamayyar jagororin Arewa ta tsakiya, ranar Alhamis, sun tabbatar da goyon bayansu ga tsohon gwamnan ya karɓi ragamar APC ta ƙasa.
Matakin shugaban ƙasa Bola Tinubu da gwamnonin APC na zaɓen Ganduje a matsayin wanda suke son ya gaji shugaban APC ya haifar da ruɗani da kace-nace tsakanin mambobi.
Yayin da wasu ƙusoshi ke ganin ya kamata a bar wanda zai maye gurbin Adamu ya fito daga jihar Nasarawa bisa tsarin raba muƙaman APC, wasu kuma sun goyi bayan zabin tsohon gwamnan Kano.
Muna goyon bayan Ganduje a matsayin shugaban riƙo - Dattawa
Da yake jawabi ga yan jarida a Abuja, shugaban wakilan dattawan APC na Arewa ta tsakiya, Mista Onoja ya ce:
"Bamu yi mamaki ba don gwamnonin APC sun mara wa Ganduje baya da kuma wasu ƙungiyoyi da suka fito suka goyi bayan ya karɓi shugabancin jam'iyya na riko."
"Mu a matsayin wakilan dattawan jam'iyya na Arewa ta tsakiya, mun bi sahu wajen goyon bayan Abdullahi Ganduje. Muna goyon bayan ya ɗora daga inda Abdullahi Adamu ya tsaya."
Jam'iyyar APC Ta Sanya Ranakun Gudanar da Manyan Taruka Guda 2
A wani rahoton kuma Jam'iyyar APC mai mulki ta sanya ranar taron masu ruwa da tsaki da taron majalisar zartarwa (NEC) ta ƙasa.
Mukaddashin sakataren APC na ƙasa, Mista Festus Fuater, ya sanar da cewa tarukan biyu zasu gudana a ranakun 2 da 3 ga watan Agusta, 2023.
Asali: Legit.ng