Fitaccen Malamin Addini Ya Yi Gagarumin Hasashe Game Da Ministocin Shugaban Kasa Tinubu
- Primate Elijah Ayodele, shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, ya ce babu ko daya daga cikin sabbin zababbun ministoci da zai yi wata mu'ujiza
- Malamin addinin ya ce yan Najeriya na bukatar kara kusantar Ubangiji a wannan lokacin domin mafarkinsu ya zama gaskiya
- Ku tuna cewa shugaban kasa Tinubu ya mika sunayen ministoci 28 gaban majalisar dattawa a ranar Alhamis, 27 ga watan Yuli, domin cike wa'adin da kundin tsarin mulki ya diba
Primate Elijah Ayodele, shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, ya bayyana abun da Allah ya nuna masa dangane da wadanda shugaban kasa Bola Tinubu ya zaba domin zama ministocinsa.
A cikin bidiyon da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Juma'a, 28 ga watan Yuli, malamin addinin ya ce babu ko daya daga cikin ministocin da zai yi wata mu'ujiza da zaran ya isa ofis kuma cewa kasar na bukatar kara kusantar Allah.
Yadda Shugaban kasa Tinubu ya bayyana ministocinsa
A ranar Alhamis, 27 ga watan Yuli ne shugaban kasa Bola Tinubu ya mikawa majalisar dattawa sunayen ministocinsa 28 ta hannun shugaban ma'aikatansa kuma tsohon kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jim kadan bayan Gbajabiamila ya gabatarwa yan majalisar da sunayen sai shugban majalisar dattawan, Godswill Akpabio ya karanto su.
Hakazalika majalisar ta sanar da cewar za a fara tantance ministocin a ranar Litinin, 31 ga watan Yuli, yayin da yan majalisar suka dakatar da hutunsu na shekara domin tantance dukkanin mutanen da aka zaba.
Nau'in mutanen da ke cikin jerin ministocin Shugaba Tinubu
Masana harkokin siyasa da dama sun yabawa wannan jerin sunayen, inda suka jinjinawa shugaban kasar kan yadda ya tabbatar da sako matasa da mata a ciki.
Nazari da aka yi kan rukunin ministocin farko da aka gabatar ya nuna cewa mata bakwai aka zaba, wanda ya kasance kaso 25 cikin dari da sunayen da aka gabatar, kuma uku daga cikinsu suna kasa da shekaru 40.
Sai dai kuma Ayodele a cikin sabon bidiyon hasashensa, ya ce:
"Ban ga kowani minista da zai yi mu'ujiza a wannan gwamnati ba. Gwamnatin na bukatar neman taimakon Allah domin ya inganta abubuwa a kasar nan."
Ga wallafarsa a kasa:
Jerin jihohi 11 da basu samu ministoci ba
A wani labarin kuma, mun kawo a baya cewa Shugaban kasa Bola Tinubu ya mika sunayen ministoci 28 zuwa majalisar dattawa a ranar Alhamis, 27 ga watan Yuli domin tantance su.
Bayan an dangata gaba daya sunayen da ya mika majalisa da jihohinsu na asali, an gano cewa wasu jihohi 11 basu samu kujerun ministoci ba tukuna.
Asali: Legit.ng