Tsohon Bidiyon Wike Yana Cewa Ba Zai Yi Minista Ba Ya Tada Kura A Intanet
- Tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike na daga cikin jerin ministocin da Bola Tinubu ya mika majalisa a jiya
- Wike wanda dan jam'iyyar PDP ne, ya goyi bayan Shugaba Tinubu yayin zaben shugaban kasa a watan Fabrairu
- An bankado wani faifan bidiyo da aka gano Wike na alfaharin cewa ba zai karbi mukamin minista a jihar ba
FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya mika sunayen ministoci 28 ga majalisar Dattawa a jiya Alhamis 28 ga watan Yuli.
Majalisar ta sanar da sunayen ministocin ga 'yan Najeriya da ke dauke da tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, Legit.ng ta tattaro.
Bayanin Wike a cikin faifan bidiyo akan mukamin minista
Bayan fitar da sunayen ministocin, an dauko wani faifan bidiyo da aka gano tsohon gwamnan Rivers, Nyesom Wike na cewa ba shi da niyyar zama minista.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya kara da cewa a matsayinsa na wanda ya kammala wa'adi biyu akan kujerar gwamnan Rivers mai arziki, babu abinda zai yi da minista.
Wike ya bayyana cewa mutum daya ake bukata a jiha a matsayin minista don haka ba zai zama minista ba.
Ku kalli faifan bidiyon da Daily Trust ta wallafa:
A cewarsa:
"Mutum daya ne kadai zai zama minista a jiha, ba zan zama minista ba, ba zai yiyu ba.
"Ni ba ci ma zaune ba ne, jihar Rivers na da arziki, idan ba ka son cin zabe, wannan kai ta shafa.
"Ba ni nake gudanar da zabe ba, duk wanda ya saka takalmi, shi ya san inda yake matse shi."
Tsoffin gwamnonin da suka samu mukamin minista
Sauran tsoffin gwamnonin da ke cikin ministocin akwai tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai da na Jigawa Badaru Abubakar da kuma na Ebonyi, Dave Umahi.
Kace-Nace Yayin Da 'Yan Najeriya Suka Soki Yadda Tinubu Ya Zabi Ministoci, Sun Bayyana Abin Da Ya Kamata
Tsohon Gwamna, Nasiru El-rufai da Nyesom Wike na daga cikin wadanda suka taba rike mukaman ministoci a shekarun baya, cewar Daily Post.
Mukamin Minista: “A Karshe, Yan Najeriya Za Su Ji Dadi”, Omisore Ya Ba Da Tabbaci
A wani labarin, sakataren jam'iyyar APC, Iyiola Omisore ya ba da tabbacin cewa tsohon Gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers ka iya firowa a jerin ministoci.
Omisore ya ce ta na iya yiyuwa tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso ma ya tsinci sunansa a jerin ministocin.
Omisore ya bayyana haka ne a ranar Talata 11 ga watan Yuli a shirin siyasa na gudan talabijin na Channels.
Asali: Legit.ng