Gwamna Aliyu Ya Aika Sunayen Kwamishinoni Ga Majalisar Dokokin Sokoto
- Gwamna Ahmed Aliyu ya tura sunayen kwamishinoni 16 zuwa majalisar dokokin jihar Sakkwato ranar Alhamis
- Ya ce wannan shi ne rukuni na farko kuma ya bi duk matakan da ya dace wajen zaɓo mutanen da ya naɗa
- Shugaban majalisar ya sanar cewa zasu tantance mutanen a ranakun 2 da 3 ga watan Agusta, 2023
Sokoto state - Gwamna Ahmed Aliyu na jihar Sakkwato ya mika sunayen kwamishinoni 16 ga majalisar dokokin jihar, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.
Sunayen wadanda gwamnan ya naɗa na kunshe ne a cikin wata wasika da ya aike wa shugaban majalisar, Alhaji Tukur Bala, kuma ya karanta wa mambobi a zauren majalisar ranar Alhamis.
Gwamnan ya ambaci tanadin sashe na 192 da sauran sassan da suka dace na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na 1999 da aka yi wa kwaskwarima kan nadin kwamishinoni.
Ya ce nadin mutanen 16 ya biyo bayan tuntuba da kuma bin matakan da suka dace kamar yadda yake kunshe a cikin dokokin aikin gwamnati.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A rahoton Ripples, Gwamna Aliyu ya ce:
“Wannan naɗin kwamishinoni 16 shi ne rukunin farko kuma ya biyo bayan bukatar kafa majalisar zartarwa ta jiha kamar yadda yake ƙunshe a dokokin aikin gwamnati."
Majalisa ta sanya ranakun tantance sabbin kwamishinonin
Shugaban majalisar ya sanar da sauran mambobi cewa majalisar gaba daya za ta yi aikin tantance waɗanda aka zaba a ranakun 2 da 3 ga watan Agusta, 2023.
Jerin sunayen mutanen da gwamna Aliyu ya aika wa majalisa
Legit.ng Hausa ta tattaro muku jerin sunayen sabbin kwamishinonin da gwamna Aliyu ya aika zuwa majalisar dokoki, ga su kamar haka:
1. Tukur Alkali
2. Bala Kokani
Kace-Nace Yayin Da 'Yan Najeriya Suka Soki Yadda Tinubu Ya Zabi Ministoci, Sun Bayyana Abin Da Ya Kamata
3. Aminu Abdullahi
4. Mohammed Shagari
5. Nasiru Aliyu
6. Ya’u Danda
7. Yusuf Maccido.
8. Jamilu Gosta
9. Bashar Umar
10. Dakta Jabir Mai-Hulla
11. Balarabe Kadadi
12. Isa Tambagarka
13. Aliyu Tureta
14. Hadiza Shagari
15. Asabe Balarabe
16. Bello Wamakko.
Bayan Tsawon Lokaci, An Bayyana Sunan Sabon Shugaban Jam'iyyar APC
A wani labarin na daban kuma Barista Idris Shu'aibu ya samu nasarar zama sabon shugaban APC ta jihar Adamawa bayan taron kwamitin SEC.
Tsohon shugaban, Ibrahim Bilal ya rasa muƙaminsa ne kan zargin karkatar da kuɗaɗen jam'iyya a 2022.
Asali: Legit.ng