Dalilan da Suka Jawo Babu Minista ko 1 Daga Kano, Filato da Legas a Sahun Farko
- Duk abin da ake yi, akwai jihohin da har yanzu ba su san wadanda za su zama Ministocinsa ba a FEC
- Jihohin nan sun hada da Kano inda aka ja daga tsakanin ‘Yan Kwankwasiyya da mutanen Ganduje
- Sabanin siyasa da shari’ar da ba a gama a kotun zabe ba, sun yi tasiri wajen gaza zakulo Ministoci 36
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abuja - A yayin da aka aika sunayen Ministoci zuwa majalisar tarayya, akwai jihohin da har zuwa yanzu ba su da wakilci idan aka tashi rantsar da FEC.
Ganin haka, Daily Trust tayi bincike game da abin da ya jawo wasu jihohi irin Kano, Adamawa, Legas, Gombe da sauransu, ba su da kowa a jerin farko.
Abin da ya faru a Kano bai rasa nasaba da Abdullahi Ganduje wanda ake burin ya zama shugaban APC, kuma ana kokarin jawo su Rabiu Kwankwaso.
Ciwon kan Kwankwasiyyya da Gandujiyya
Rabiu Kwankwaso ya yi takarar shugaban kasa a NNPP, sannan jam’iyyarsa ta karbe mulkin jihar Kano wanda har yau ana shari’a da APC a kan zaben.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wani jigo a APC ya ce daga Kano akwai su A.T Gwarzo wanda sun dade da Tinubu, sannan Rabiu Bichi da Abdulrahman Dambazau na neman Minista.
A Legas kuwa, rahoton ya ce an rasa wanda zai dauka ya yi Minista tsakanin Babatunde Fashola, Tokunbo Abiru, Akinwunmi Ambode da Dayo Israel.
‘Umaru Dan Adda’, Gwamna ko Kyari
A dalilin rikicin siyasar Gombe, Bola Tinubu bai iya nada kowa ba. Da farko shugaban Najeriyan ya so dauko amininsa wani ‘dan kasuwa, Umar Abdullahi.
Gwamna Inuwa Yahaya kuwa yana so ne a tafi da tsohon hadiminsa, Abubakar Inuwa Kari. A gefe guda ana duba gudumuwar Jamilu Gwamna ga APC.
A Filato, jaridar ta ce APC ta bada sunayen Simon Lalong, Rufus Bature da Farfesa Dakas C. Dakas, amma ba a zabi kowa ba, watakila saboda ana kotu.
Eno ya ga ranar janye kara a kotu
A Kuros Riba, yaran Ben Ayade ba su ji dadi ba da jin dauko Dr. Betty Edu da Sanata John Owan-Eno ba, amma aka yi watsi da tsohon Gwamnan Jihar.
Sanata Ahmad Lawan da Hon. Bashir Sheriff Machina ake tunanin za a zaba daga Yobe. Ko da Machina ya yaki APC, ya dade da Tinubu a tafiyar siyasa.
Shi ma Lawan ya rasa shugabancin majalisa, amma ya yi takara da shugaban kasar a APC.
Bola Tinubu bai gama nadi ba
Mun ji labari za a fitar da sunayen karin mutane fiye da 10 da za su samu kujerar Ministoci, sai Majalisar dattawa ta fara shirin karbar wata wasika.
Bayanin Femi Gbajabiamila ya nuna akwai yiwuwar kirkiro sababbin ma’aikatu dabam domin a iya tafiya da wadanda za a ba mukamai a gwamnatin.
Asali: Legit.ng